1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariár Anfal ga mukarraban Saddam Hussaini

A T BalaJanuary 8, 2007
https://p.dw.com/p/Btwk
Zaman kotu a Bagadaza
Zaman kotu a BagadazaHoto: AP

Shariár ta yau wadda ke zama mataki na biyu na tuhumar da akewa manyan muƙarraban Saddam kuma shugabannin jamíyar Baath a dangane da kisan gilla ga kurdawa 180,000 da aka yiwa laƙabi da farmakin Anfal, a yayin zaman shariár alkalin kotun Mohammed al-Oreibi ya soke dukkan wata tuhuma a dangane da wannan kara ga Saddam Hussaini wanda tuni aka zartar masa da hukuncin kisa a ranar 30 ga watan Disamba bisa laifin kisan yan shiá 148 a garin Dujail. Hukuncin da ya haifar da damuwa da cece-kuce a tsakanin alúmomin duniya.

Mai shariár yace kotun ta sami takarda daga babbar kotun koli ta kasar Iraqi a ranar 7 ga watan Janairu a game da kisan Saddam a saboda haka yace bisa ga tanadin sashi na 304 na kundin tsarin mulikin Iraqi an ajiye dukkan tuhuma da suka shafi Saddam a game da wannan sharia.

Daga nan ne kuma mai gabatar da kara ya yi kiran sauran mutane shida da ake tuhuma daya bayan daya wadanda suka hada da Ali Hassan al-Majid wanda aka fi sani da suna Chemical Ali wanda dan uwa ne ga Saddam Hussaini kuma tsohon Ministan tsaro na kasar Iraqi.

Hassan al-Majid wanda ke da alamar gajiya yaki zama a kujerar sa, wadda a bisa aláda take bayan kujerar da Saddam kan zauna a yayin da suka baiyana a kotu. Ali al-Majid ya kafe yana mai karanta wasu ayoyi daga cikin alkurani mai tsarki, Ganin wannan takaddama mai shariá al-Uraibi ya yi umarni da kakkausar murya ga jamian kotu su sanya al-Majid ya zauna a kan kujerar.

Shi dai Ali Hassan al-Majid shi ne mutumin da ake gani jagoran da ya dabbaka farmakin soji a kan kurdawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 180,000 yawancin mutanen ana zargin an kashe su ne ta hanyar sanya musu iska mai guba.

Dukkanin mutane bakwai da ake zargi da hannu a shariár ta Anfal da suka hada da marigayi Saddam Hussaini sun ki amsa laifin da ake zargin su da ita ta kisan kare dangi.

Da dama daga cikin alúmar Kurdawa na baiyana takaici cewa babban mutumin da suke tuhuma da laifi wato Saddam, Hussaini ba zai fuskanci wannan hukunci ba a sabili da rataye shi da aka yi a shariár da aka yi masa ta kisan yan shiá 148 a tsakanin shekaru 1980.

A cewar wani dattijo mai shekaru 60 da haihuwa dake garin Arbil a arewacin Iraqi, Saddam ya mutu amma taasar Anfal da ya aikata bai gushe ba. Masu gabatar da kara sun mika wasu takardu dake danganta Ali al-Majid da sauran mutanen da ake tuhuma da farmakin na Anfal.

Idan aka tabbatar da laifin da ake tuhumar su akai dukkanin mutanen shida za su fuskanci hukuncin kisa. Kurdawa da dama sun gabatar da shaida inda suka baiyana yadda dubban jamaá maza da mata da kananan yara aka gana musu azaba a zamanin Saddam wadda ta kai su ga rasa rayukan su.

A waje guda kuma mai baiwa P/M Iraqi shawara kan alámuran tsaro Mowafaq al- Rubaie ya bukaci alúmar kasar Iraqi da cewa zamanin Saddam ya riga ya wuce su hada kai domin ciyar da kasar gaba.