1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Kasashen Duniya

Mohammad Nasiru AwalOctober 27, 2003
https://p.dw.com/p/BvqR

Taron ba da taimakon kudi ga kasar Iraqi a birnin Madrid da mika wuya da Iran ta yi dangane da batun nukiliya na daga cikin muhimman batutuwa da suka daukar hankalin jaridun kasashen ketare a karshen makon jiya. To amma da farko zamu fara ne da sharhi akan lamuran siyasa a nan Jamus musamman dangane da shirin yiwa tsarin fansho kwaskwarima.

Jaridar Standard ta birnin Vienna can kasar Austria ta kwatanta shirin na gwamnatin Schröder da wani aikin tiyata na gaggawa. Tana mai cewa shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder yayi daidai da ya kwatanta shirinsa na yiwa tsarin fansho garambawul a matsayin wani tubali na tabbatar da ci-gaban tsarin tallafawa tsofaffi. Bugu da kari Schröder da jam´iyun kawance karkashin jagorancin jami´yarsa ta SPD sun nuna karfin zuciya wajen sakarwa ´yan fansho daukar wannan nauyi.

Ita kuwa jaridar La Republica ta birnin Rom din Italiya bayyana wannan shiri ta yi da cewa babban koma-baya ne ga tsarin fansho na gwamnatin kawance tsakanin jam´iyun SPD da Greens. Jaridar ta ce matakin da gwamnatin Schröder ta dauka, zai yi mummunar illa ga rayuwar tsofaffi kimanin miliyan 19.5 da suka yi ritaya daga aiki. Yanzu kuma sai birnin Madrid, inda a karshen mako aka kammala taron neman kudin sake gina kasar Iraqi.

A cikin sharhin da ta yi jaridar kasar NL wato De Volkskrant ta bayyana rashin gamsuwa ga sakamakon taron, duk da alkawuran da manyan kasashen duniya suka dauka na ba da taimakon kudin sake gina Iraqi. Jaridar ta ce duk da makudan kudaden da wannan taro ya tara, hakan bai kai adadin da ake bukata ba. Daukacin kasashe masu ba da tallafin dai na adawa da ba da taimakon kudi amma a hannu daya a hana su damar fadar yadda za´a kashe wadannan kudade. Jaridar ta kara da cewa taron na birnin Madrida ya nuna a fili cewa har yanzu da akwai baraka tsakanin Amirka da sauran kasashen duniya dangane da batun kasar Iraqi, ko da yake an dan samu ci-gaba fiye da watannin baya.

Ita kuwa jaridar Salzburger Nachrichten ta mayar da hankalinta ne akan amincewar da kasar Iran ta yi na ba hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa hadin kai game da shirin ta na nukiliya da ake kace-nace akai. Jaridar ta ce yanzu dai an kusa gane gaskiyar dake akwai game da ikirarin da Iran ta yi cewa ba ta da wani shiri a boye na kera makaman nukiliya. Jaridar ta ce yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai da mahukuntan birnin Teheran babban ci-gaba ne wajen rage hauhawar tsamari a wannan yanki. To sai dai a ko-wane lokaci wannan yarjejeniyar ka iya rugujewa, wanda hakan zai janyo tserereniyar kera makaman nukiliya a yankin GTT.

Ita ma jaridar New York Times ta yi tsokaci akan wannan batu tana mai cewa Iran ta dauki wani muhimmin mataki wajen bayyana shirinta na nukiliya a fili. Jaridar ta ce idan aka aiwatar da wannan matakin to hankalin duniya zai kwanta musamman game da damuwar da ake nunawa na kera makaman nukiliya a Iran. Jama´a da wannan sharhi na jaridar New York Times muka kawo karshen sharhunan jaridun kasashen duniya.