1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka

Mohammad Nasiru AwalJune 3, 2005

Jaridun sun rubuta sharhuna da dama akan nahiyar Afirka a wannan mako daga 30 ga mayu zuwa 3 ga yuni.

https://p.dw.com/p/BvpE
Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe
Shugaba Robert Mugabe na ZimbabweHoto: AP

Jama´a barkanku da warhaka. To a yau shirin zai fara ne a birnin Cape Town na kasar ATK inda a ranar laraba da ta gabata aka bude babban taro game da tattalin arzikin duniya, inda a wannan karon taron ya fi mayar da hankali kan nahiyar Afirak. A cikin sharhin da ta rubuta jaridar Frankfurter Allg. Zeitung ta fara ne da tambayar cewar shin wani shiri ne ya fi dacewa wajen tallafawa Afirka a fannin tattalin arziki? Shin sabon kawance nan ne na raya kasashen Afirka wato NEPAD ko kuma shirin Marshalplan ake bukata yanzu kamar yadda FM Britaniya Tony Blair ya ba da shawara? Taron na birnin Cape Town na samun halarcin wakilai sama da 700 na kamafanoni da gwamnatocin kasashe 42. Taron na matsayin share fagen taron kolin kungiyar G-8 da za´a yi a ´yan makonni kalilan masu zuwa a yankin Scotland karkashin jagorancin Britaniya. Babban jigo taron kolin dai zai hada har da tattaunawa akan gagarumin shirin FM Blair na bawa Afirka karin taimakon dala miliyan dubu 25 a cikin shekaru 5 masu zuwa. To amma abin tambaya inji jaridar ta FAZ shine mene ne makomar shirin NEPAD a yanzu, shin an yi watsi da shi ne ko kuma wani sabon yunkuri ake yi ne don yin fatali da shirin NEPAD, wanda shugabannin Afirka suka kirkiro da nufin samun hanyoyin fid da Afirka daga kangin wahalhalu iri daban-daban da nahiyar ke fuskanta. Ko shakka babu Afirka na bukatar taimako ta kowane fanni daga kasashen duniya mafiya arziki, to amma ba daidai bane a rika gabatar da sabbin shirye-shirye ba tare da an ga makwancin na farko ba. Ita ma jaridar TAZ ta rubuta sharhi game da taron na Cape Town tana mai cewa yanzu lokaci yayi da kasashe masu arziki zasu cika alkawuran da suke dauka wajen tallafawa Afirka, musamman a ayyukan raya kasa, yafe basussuka tare da taimakawa a kafa gwamnatoci na gari masu adalci ga talakawan Afirka.

A wani sabon sharhi da ta rubuta har wayau jaridar TAZ ta rawaito kamfanin hakan zinari na biyu mafi girma a duniya wato AngloGold Ashanti na amsa cewar ya dade yana biyan makudan kudade don samun kariya daga daya daga cikin kungiyoyin ´yan tawaye yankin Ituri na JDK. Ko da yake hakan ya faru tun a cikin shekara ta 2004 zuwa farkon wannan shekara amma sai yanzu bayan da kungiyar kare hakkin bil Adam ta Human Rights Watch ta fallasa wannan abu sannan kamfanin na AngloGold Ashanti ya amsa cewar lalle ya kan ba da toshiyar baki da ya kai dala dubu 30 ga sojojin sa kai na kungiyar FNI don ya tafiyar da aikin hakan gwal a yankin arewa maso gabashin Kongo.

Ita kuwa jaridar FR ta mayar da hankali akan halin da ake ciki a Ivory Coast inda ta ce yanzu haka dai shirin wanzar da zaman lafiyar kasar ya shiga mawuyacin hali, sakamakon kisan gillan da aka yiwa mutane 41 a kusa da garin Doueke dake yammacin kasar. Jaridar ta ce wannan yanki ya kasance dandalin tashe tashen hankula da zub da jini tsakanin kabilar Guere ´yan asalin yankin da kuma musulmi wadanda suka yi kaura daga arewacin Ivory Coast. Jaridar ta ce irin wannan ta´asa na janyo koma baya ga shirin kwance damarar sojojin sa kai, da aka yi niyar kammalawa a ranar 27 ga wannan wata sannan an gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 30 ga watan oktoba.

Bari mu kammala shirin da sharhin da jaridar SZ ta rubuta game da matakan rushe gidajen talakawa da gwamnatin Zimbabwe karkashin shugaba Mugabe ta dauka. Jaridar ta ce wannan mataki zai kara jefa talakawan kasar cikin mummunan hali na talauci. Jaridar ta ce a daidai lokacin da kashi 8 cikin 10 na al´umar Zimbabwe ke fama da matsanancin talauci kuma ba sa samun abin sakawa bakin salati, sai shugaba Mugabe yayi odar sabbin jiragen saman yaki guda 8 daga kasar Sin.