Sharhunan Jaridu | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhunan Jaridu

Sharhunan jaridun Jamus akan Afurka

default

Mwai Kibaki da Kofi Annan da Raila Odinga


Kenya/Somaliya/Afurka ta Kudu


Kamar dai yadda aka saba a wannan makon mai karewa ma jaridu da mujallun Jamus sun zagaya sassa daban-daban na nahiyar Afurka domin tsegunta wa masu karatu ire-iren abubuwan dake faruwa a wannan nahiya a fannoni na siyasa, tattalin arziki da zamantakewa. Amma da farko zamu fara ne da ya da zango a ƙasar Kenya, wadda a wannan makon tsofon sakatare-janar na Majalisar Ɗunkin Duniya Kofi Annan ya kai mata ziyara a karkashin wani yunkuri na neman dinke barakar da ta biyo bayan zaben kasar da aka gudanar watan desemban da ya gabata take kuma neman yi wa al'amuran siyasa da tattalin arzikin kasar mummunan tabo. Jaridar Der Tagesspiegel tayi bitar wannan yunkuri inda take cewar:


Kenya

"Kofi Annan dai ba shi ne jami'in farko da ya nemi dinke barakar da siyasar kasar Kenya ke fama da ita a halin yanzu ba. Amma dukkan yunkurin da aka gabatar gabaninsa bai yi nasara ba. Matsalar tana da sarkakiyar gaske, duk da cewar shugaban 'yan hamayya Raila Odinga, a wannan makon yayi tayin shiga a dama da shi a gwamnati bisa sharadin da suka cimma tare da Kibaki a shekara ta 2002, wanda Kibakin bai cika ba. Wannan sharadin ya tanadi ci gaban Kibaki da zama shugaban kasa, a yayinda shi kuma Odinga zai rike mukamin P/M mai cikakken iko. Muddin Kofi Annan bai samu nasarar warware rikicin a cikin ruwan sanyi ba, to kuwa kasar Kenya ka iya fadawa cikin wata matsala mafi muni akan abubuwan da suka wakana a kasar kwanan baya."

Ita kuwa mujallar Stern, a ra'ayinta su kansu 'yan kasar ta Kenya ne ya kamata su nemi bakin zaren warware wannan mummunan rikicin ta ba su taba shaida irin shigensa ba tun bayan samun 'yancin kansu. Mujallar ta kara da cewar:

"Kenya na cikin wani hali mafi muni tun bayan samun 'yancin kanta. Kuma wannan yamutsin abin mamaki ne ganin yadda aka dade ana yaba mata da kasancewa wani dandalin zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin kasashen gabacin Afurka hade da kyakkyawan cudwe-ni-in-cude-ka tsakanin kabilunta su kimanin 42. A hakika dai ba kowa ne musabbabin wannan rikici da ta samu kanta a ciki ba illa jami'an siyasarta, wadanda a yanzun alhakin dinke wannan baraka ya rataya a wuyansu."

Somalia

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon ta fi mayar da hankalinta ne akan matsalar 'yan gudun hijira dake addabar gabacin Afurka, inda take cewar:

"Matsalar 'yan gudun hijira sai dada yin tsamari take yi a gabacin Afurka, kuma galibi 'yan kasashen Somaliya da Habasha ne. Wannan matsalar kuwa tun ba yau ba ne ta fara, inda a halin yanzu haka aka kiyasce cewar kasar Yemen na karbar bakoncin 'yan gudun hijirar Somaliya kimanin dubu 800. To sai dai kuma a yanzun an fara fuskantar zaman dardar tsakanin 'yan gudun hijirar da al'umar Yemen dake zarginsu da fashi da karuwanci da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi da cinikin sauran abubuwa masu sa maye. Amma fa matsawar da kasar Somaliya ba ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba, Yemen zata ci gaba da fama da tuttuɗowar 'yan gudun hijira daga Somaliyar."

Afurka ta kudu

Kasar Afurka ta Kudu dake shirye-shiryen karbar bakoncin gasar kwallon kafa ta kofin duniya a shekara ta 2010 tana fama da karancin wutar lantarki, lamarin da ya sanya ake fargabar cewar wannan matsala ka iya kawo cikas ga wasannin da za a gabatar a kasar nan da shekaru biyu masu zuwa, a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Kwararrun masana sun bayyana cewar kasar Afurka ta Kudu zata ci gaba da fama da matsalar karancin wutar lantarki a cikin shekaru biyar zuwa bakwai masu zuwa. A halin yanzu haka mutane sun fara ba'a game da cewar za a gudanar da wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya ne a cikin dufu. A wasannin cin kofin duniya na kewallon rugby da aka gudanar a kasar shekarar da ta gabata sai da hukumar wutar lantarki ta kasar ta yi kira ga jama'a da suyi taka tsantsan wajen amfani da wutar saboda gudun daukewarta a daidai lokacin da Afurka ta Kudun take wasa na gaba da na karshe."