1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhuna kan Dangantakar Afurka da Turai

Ahmad Tijani LawalDecember 14, 2007

Turai da Afurka a taron Lisbon

https://p.dw.com/p/Cbsl
Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe da Angela Merkel ta JamusHoto: AP

EU/Afrika/Zimbabwe

To hatta a wannan makon ma dangantakar kasashen Turai da na Afurka ita ce tafi daukar hankalin masharhanta na jaridu da mujallun Jamus tare da ba da la’akari da taron kolin sassan biyu da aka gudanar a Lisbon makon da ya gabata. A lokacin da take tofa albarkacin bakinta akan sabanin dake akwai tsakanin kasashen na Afurka da na Turai a game da yarjeniyoyin sassaucin dangantakar ciniki jari dar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“A lokacin taron kolin kasashen Afurka da na Turai makon da ya wuce, shugaban hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Afurka Alpha Oumar Konare ya fito fili ya bayyana cewar faufau kasashen Afurka ba zasu amince da sabbin yarjeniyoyin cinikin da kasashen Turai suka gabatar ba, wajibi ne a sake bitarsu dalla-dalla. Amma fa ga alamu kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ba su da irin wannan ra’ayi na sake tattauna yarjeniyoyin, illa kawai a yi musu gyaran fuska, inda suka ce kasashen Afurka ne zasu ci gajiyar wadannan yarjeniyoyi, in har amince da su kuma da wuya su janye daga wannan matsayi nasu.”

EU-Afrika

Ita kuwa jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta mayar da hankali ne akan korafin da kungiyoyin taimako masu zaman kansu kamar su Oxfam suka yi dangane da shawarar da hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Turai ta bayar, inda ta ce:

“Bisa ga ra’ayin kungiyoyi masu zaman kansu Kungiyar Tarayyar Turai na kokari ne kawai domin ganin kasashenta sun samu shigar da kayayyakinsu kasuwannin kasashen Afurka da Karibiya da Pacifik a cikin sauki da araha da kuma karya alkadarin masana’antun kasashen tun kafin su samu kafar tsayawa kan kafafuwansu.”

Zimbabwe

A cikin nata sharhin jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi bitar dangantakar kasashen Turai ne da shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe, inda take cewar:

“An dade ba gamaciji tsakanin Robert Mugabe da kasashen Turai, saboda matsin lambar da kasashen ke wa gwamnatinsa, lamarin da a hakika yake taimakawa wajen gurbata yanayin dangantaku tsakanin kasashen Turai da na Afurka. Wani abin da ya bata wa shugabannin Afurka rai ma shi ne yadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki lamrin shugaba Mugabe da sunan Kungiyar Tarayyar Turai.” Jaridar ta SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta ce ba yadda za a yi a tafiyar da wata dangantaka ta siyasa mai ma’ana akan irin wannan turba. Dukka kasashen Turai da na Afurka sun bata lokaci da yawa, wanda ya kamata da su yi amfani da shi wajen kawar da banbance-banbancen dake tsakaninsu domin bin wata manufa ta bai daya.”

Afrika

A cikin wata sabuwa kuma jim kadan bayan da taron kolin kasashen na Afurka da na Turai suka cimma daidaituwa akan wasu nagartattun matakan da zasu dauka domin tinkarar matsalar nan ta bakin haure aka samu rahoton afkuwar wani mummunan hadari wanda yayi sanadiyyar bakin haure kimanin 140 lokacin da suke kokarin shigowa nahiyar Turai ba a bisa ka’ida ba a tekun atlantika ta bahar-rum. Jaridar DIE TAGEZEITUNG ce ta ba da wannan rahoton, inda ta kara da cewar:

“Ta la’akari da irin wadannan hadarurruka dake haddasa mace-macen wadannan bakin haure dake neman shigowa Turai ko ta halin kaka, shuagabannin Turai da na Afurka, a lokacin taron kolinsu a Lisbon, suka cimma daidaituwa akan kara karfafa matakansu domin magance wannan matsala ta bakin haure. A wannan shekarar kimanin bakin haure 11 da 400 daga nahiyar Afurka suka tsallako zuwa tsuburan Kanariya na kasar Spain a cikin kananan kwale-kwale kuma tuni aka mayar da kashi 50% daga cikinsu gida. A shekarar da ta gabata kuwa adadin ya kai dubu 31. Dubban ‘yan gudun hijirar ke asarar rayukansu kowace shekara akan wannan hadarin gaske.