1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhohin da jaridun Jamus suka yi kan nahiyar Afirka a wannan makon.

Jaridun Jamus a wannan makon, sun yi sharhohi kan btutuwa da dama da ke ci wa al’amuran siyasa da na zamantakewar jama’a tuwo a ƙwarya a nahiyar Afirka. Batun yaƙin neman zaɓe a ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, da hauhawar tsamarin da ake ta ƙara samu a Somaliya, da rikicin yankin Darfur na cikin muhimman jigogin da jaridun suka yi sharhohi a kansu dangane da nahiyar ta Afirka.

Yaƙin neman zaɓe a birnin Kinshasa na ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango.

Yaƙin neman zaɓe a birnin Kinshasa na ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango.

Da farko dai, jaridar Neue Zürcher Zeitung, ta yi sharhi ne kan zaɓen da ake shirin gudanarwa a ran 30 ga wannan watan a Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango, inda ta ce, girman ƙasar da albarkatun ƙasar da take da su, da ɗimbin yawan hanyoyin samad da makamashin da ke Kwangon, sun isa a ce ma wannan ƙasar ce ke jagorancin nahiyar Afirka. Amma abin ban takaici ne, inji jaridar, ganin cewa, Kwangon, wadda sarki Leopold na biyu na ƙasar Belgium ya mai da ita kamar abin mallakarsa a cikin ƙarni na 19, wadda kuma Belgium ɗin ta yi wa mulkin mallaka tun daga 1908, ba ta taɓa samun damar gabatad da wani shiri na inganta halin rayuwar duk ’yan ƙasarta ba. Farkon Firamiyan ƙasar, bayan samun ’yancinta daga Belgium a cikin shekarar 1960 bai ci nasarar haɗe kawunan ’yan ƙasar ba, saboda katsalandan ɗin da ƙasashen ƙetare suka yi masa da kuma rikicin cikin gida da abokan hamayyarsa na yankin Katanga mai arzikin tagulla, waɗanda ma suka nemi ɓallewa daga kasar gaba ɗaya.

Da wannan tarihin ne dai al’umman Kwangon za su ka da ƙuri’a a farkon zaɓen dimukraɗiyyan ƙasar a ran 30 ga wannan watan. Ba don angaza wa mahukuntan ƙasar da Majalisar Ɗinkin Duniya, da ƙasashen da ke ba da tallafi suka yi ba, da har ila yau ba a kai ga tsara shirye-shiryen zaɓen ba balantana ma gudanad da shi, inji jaridar.

Amma a halin yanzu, hukumar zaɓen ƙasar ta yi rajistan masu zaɓe kimanin miliyan 25 da ɗigo 7, waɗanda za su ka da ƙuri’unsu a cikin kwanaki 10 masu zuwa. Sai dai har ila yau, da akwai yamutsi a shirye-shiryen zaɓen. Yawan ’yan takara a zaɓen ma kawai, wani abu ne mai jirkitarwa. A lal misali, a mazaɓun larduna 4 da aka ware wa babban birnin ƙasar, wato Kinshasa, kusan ’yan takara ɗari 8 da 80 ne ke neman shiga majalisa. Kujerun da mazaɓun ke da su a majalisar kuwa, ba su fi 17 ba. Wato a ranar zaɓen, duk mai ka da ƙuri’a, a waɗannan lardunan na Kinshasa, sai ya binciki hotuna ɗari 8 da 80 don gano ɗan takarar da yake son zaɓa. Jariadar Neue Zürcher Zeitung dai na ganin cewa, wannan tsarin ba karamin ruɗami da jirkitarwa zai janyo ba a ranar zaɓen.

Ita ko jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi sharhinta ne kan taron da aka gudanar a birnin Brussels a ran talatar da ta wuce, don tattauna batun samo ƙarin taimako ga yankin Darfur na ƙasar Sudan. A ganin jaridar dai, taron bai cim ma manufa ba.

Har ila yau Sudan na daddage wa kiran da ake yi mata na ta amince da girke dakarun kare zaman lafiya na MajalisarƊinkin Duniya a yankin na Darfur. Ban da haka kuma babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya bukaci gamayyar ƙasa da ƙasa da ta ba da ƙarin taimakon kuɗaɗe ga rundunar kare zaman lafiya ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, wadda ta kunshi dakaru kusan dubu 7 da a halin yanzu ke girke a yankin. Jami’in kula da batutuwan tsaro na kungiyar AUn, Said Djinnit, ya faɗa wa taron na birnin Brussels cewa daga nan zuwa watan Satumba mai zuwa dai, rundunar za ta bukaci kimanin dola miliyan 50. Har ila yau kuma, za a bukaci ƙarin kuɗi na dola miliyan ɗari 2 da 70, idan rundunar za ta gudanad ayyukan kare zaman lafiyar har zuwa ƙarshen wannan shekarar, inji jami’in.

Batun hauhawar tsamarin da ake ta ƙara samu tsakanin ƙasashen Habasha da Somaliya, shi ne jigon da jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhi a kansa dangane da nahiyar ta Afirka. Jaridar na ganin cewa, lamarin sai ƙara ta’azzara yake yi. Rahotannin kafofin yaɗa labarai da dama sun tabbatar da cewa dakarun Habasha sun kutsa cikin harabar Somaliyan da tankunan yaƙi. Tun da daɗewa ne dai Habashan ta ce ba za ta ƙyale ’yan kungiyoyin islaman Somaliyan, waɗanda a halin yanzu suke riƙe da babban birnin ƙasar Mogadishu, su yi ta cin karensu babu babbaka ba, a yunƙurin da suke yi na yaɗa angizonsu zuwa sauran yankunan ƙasar. Gwamnatin birnin Addis Ababa ta ƙarfafa aniyarta ta murƙusad da ’yan isalaman na Somaliya.

Duk da musanta rahotannin da jami’an gwamnatin birnin Addis Ababa ke yi, tabbas ne cewa a halin yanzu, dakarun Habashan na girke a garin Baidoa, wato cibiyar gwamnatin wucin gadi ta Somaliya, mai samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya.

Jaridar dai na bayyana ra’ayin cewa, idan ba hankali aka yi ba, to rikicin da ƙasashen Habasha da Eritrea ke yi da juna, zai yaɗu ne zuwa Somaliyan. Yayin da ’yan tarayyar shari’ar islaman na Somaliya ke zargin gwamnatin wucin gadin ƙasar da kasancewa ’yar amshin shatan Habasha, ita gwamnatin kuma na zargin ƙasar Eritrea ne da bai wa ’yan islaman ɗaurin gindi da tallafa musu da makamai. Firamiyan gwamnatin wucin gadin ta Somaliya, Ali Mohammed Gedi, ya faɗa wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, ƙasar Eritrea na ta ci gaba da turo mayaƙa da makamai ga ƙungiyoyin islaman. Wannan zargi dai ya sa ana tantama kan yiwuwar fara shawarwarin sulhu tsakanin ƙungiyoyin islaman da gwamnatin wucin gadin, wanda aka shirya yi a ƙarshen wannan makon a birnin Khartoum na ƙasar Sudan.

 • Kwanan wata 21.07.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvPl
 • Kwanan wata 21.07.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvPl