1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhohin da jaridun Jamus suka yi a kan nahiyar Afirka a wannan makon.

YAHAYA AHMEDJuly 28, 2006

A sharhohin da suka yi kan nahiyar Afirka a wannan makon, jaridun Jamus sun takalo batutuwa da dama da suka shafi harkokin siyasa da na yau da kullum a nahiyar. Ziyarar da shugaban ƙungiyar ’yan tawayen SLA na yankin Darfur ya kai a birnin Washington da ganawar da ya yi da shgaba Bush a fadar White House na cikin jigogin da jaridun suka fi mai da hankali a kansu. Sai kuma rikicin da yake ta ƙara tsananta a ƙasar Somaliya. Batun yawan baƙin haure daga nahiyar Afirka, da ke ta ƙoƙarin shigowa ƙasashen Turai ko ta yaya na cikin al’amuran da wasu jaridun suka yi sharhohi a kansu, a wannan makon.

https://p.dw.com/p/BvPk
Mayaƙan gamayyar kotunan islama a birnin Mogadishu
Mayaƙan gamayyar kotunan islama a birnin MogadishuHoto: AP

Da farko dai, jaridar Süddeutsche Zeitung, ta dubi halin da ake ciki yanzu ne a yankin Darfur, bayan cim ma yarjejeniyar da aka yi tsakanin gwamnatin Sudan da ƙungiyar ’yan tawayen SLA, da kuma ziyarar da shugaban ƙungiyar ’yan tawayen Minni Minnawi, ya kai a fadar White House a ran larabar da ta wuce.

A cikin sharhinta jaridar cewa ta yi:-

Babu shakka, an ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya kan yankin Darfur, kuma an rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar. Amma takardar ba ta da wata daraja. Amirka ma, wadda ta angaza wa ɓangarorin har suka sanya hannu kan yarjejeniyar, tana sane da haka. Saboda har ila yau, ana ci gaba da fafatawa a yankin na Darfur. A wasu wuraren ma, sai a ce al’amura sun ƙara tsamari ne bayan ƙulla yarjejeniyar. Shugaba Bush dai, a halin yanzu, yanna neman wata madafa ne ta nuna wa duniya cewa, yarjejeniyar tana aiki. Dalilin da ya sa ke nan ya gayyaci shugaban ’yan tawayen Sudan ɗin, Minni Minnawi zuwa fadar White House.

Shi dai Minnawi, shi kaɗai ne, a madadin ƙungiyarsa, ya sanya hannu kan yarjejeniyar da aka cim ma a birnin Abuja, inji jaridar. Sauran ƙungiyoyin, sun ƙi amincewa da yarjejeniyar, saboda a nasu ganin, ba ta tanadi komai ba na samad da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin. A sansanonin ’yan gudun hijiran Darfur ɗin ma sai da aka yi zanga-zangar ƙin amincewa da yarjejeniyar. Matakin da Amirka ta ɗauka na goyon bayan wani reshen ƙungiyar ’yan tawayen SLA kawai a yankin Darfur, ya faɗaɗa ɓarakar da ke tsakaninta da sauran ƙungiyoyin.

Jaridar Frankfurter Rundschau kuma, ta dubi hauhawar tsamarin da ake samu ne a ƙasar Somaliya, inda ake ma hasashen cewa, wani mummunan yaƙi zai iya ɓarkewa tsakanin ƙasar da Habasha. Shugabannin gamayyar kotunan islama da suka kame birnin Mogadishu, suke kuma mulki a nan, sun zargi gwamnatin Habashan ne da tura dakarunta zuwa birnin Baidoa don mara wa gwamnatin wucin gadin ƙasar Somaliyan baya. Amma ita gwamnatin birnin Adis Ababa, tana watsi da wannan zargin. Kazalika gwamnatin wucin gadin Somaliyan ma na ƙaryata labarin shigowar dakarun Habasha a ƙasar. Duk hukumomin biyu dai na nanata cewa dakarun da ake gani kamar na Habasha an birnin Baidoa, wato sojojin gwamnatin wucin gadin ne. Sai dai suna sanye da rigunan sojin Habshan ne, saboda ba su da nasu na kansu; kuma waɗannan da suke sanye da su, tsoffin riguna ne da gwamnatin Habashan ta ba su kyauta, wato kamar taimako.

Amma jaridar Frankfurter Rundschau ta ce ba haka lamarin yake ba. Tabbas ne cewa dakarun Habasha sun kutsa cikin Somaliyan, abin da masharhanta ke ganin zai iya janyo kasadar ɓarkewar wani sabon yaƙi kuma a yankin na ƙahon Afirka. Jaridar ta ƙara da cewa, jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya sun tabbatar da kutsawar dakarun Habasha dubu 5 cikin Somaliyan, tare da manyan makamai da motocin soji kusan ɗari da kuma jiragen sama masu saukar ungulu da dama. Duk waɗannan kayayyakin yaƙin dai, gwamnatin wucin gadi ta shugaba Abdullahi Yusuf, ba ta da su.

Gamayyar kotunan islaman dai na da shirin kawo duk ƙasar Somaliyan ne ƙarƙashin ikonta, bayan da ta kame babban birnin wato Mogadishu daga hannun madugan yaƙi. Farkon burinta a halin yanzu kuwa, shi ne hamɓarad da gwamnatin wucin gadin. Girke dakarun Habasha a Baidoan dai ya hana mayaƙan islaman afka wa garin. Amma shugabansu, Sheikh Hassan Ɗahir Aweys, ya yi kira ga ƙaddamad da jihadi kan Habasha, inda ya jaddada cewa, za su yi amfani da duk wata hanya wajen kare ’yan ƙasar Somaliya daga masu kawo musu hari.

Idan dai ba a yi hankali ba, inji Frankfurter Rundschau, to duk yankin na ƙahon Afirka zai iya kasancewa cikin wani mummunan rikici, saboda yayin da Habasha ke ɗaure wa gwamnatin wucin gadin Somaliyan gindi, maƙwabciyar Habashan, wato Eritrea, ita ma tana mara wa ƙungiyoyin islaman baya, tare da ba su makamai.

Haɓakar yawan baƙin hauren da ake samu daga nahiyar Afirka, masu yunƙurin shigowa nahiyar Turai cikin ƙananan kwale-kwale da kuma irin asarar rayukan da ake samu a wannan yunƙurin, su ne batutuwan da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung da Neue Zürcher Zeitung suka yi sharhi a kansu. A ganin Frankfurter Allgemeine Zeitung dai, matakan tura jami’an tsaron iyakar bakin tekun ƙasar Spain da Firamiyan ƙasar Zapatero ya ba da sanarwar ɗauka, don rage yawan bakin hauren da ke shigowa ƙasar ta jiragen ruwa, ba su cim ma manufa ba. A ƙarshen makon da ya gabata kawai, inji jaridar, sai da ƙananan jirage ɗauke da baƙin haure ɗari 2 da 48 daga nahiyar Afirka, suka isa a tsibirin Canaries da ke ƙarƙashin mulkin Spain ɗin. Ɗaya daga cikin baƙin hauren, ya mutu kafin isan jiragen a tsibirin; ɗaya kuma ya mutu a asibiti, a kan tsibirin Teneriffa. A halin da ake ciki kuma, wani jirgin ruwan ƙasar Spain ɗin, da ya ceto wasu ’yan Afrika guda 90 daga nitsewa cikin kwalekwalensu a gaɓar tekun yammacin Sahara, na nan ya rasa inda zai sauke baƙin hauren. Ƙasar Maroko, wadda ta fi kusa da inda aka ceto su, ta ƙi karɓarsu da ba da uzurin cewa ba ’yan ƙasarta ba ne. Yanzu dai kyaftin ɗin jirgin na ƙoƙarin kai su ƙasar Murteniya. Idan nan ma ba a karɓe su ba, to ba shi da wani zaɓi kuma, face ya kai su kan tsibirin Canaries, inda tun farkon wannan shekarar, baƙin haure dubu 12 daga Afirka ne mahukuntan tsibirin suka ce sun iso nan, waɗanda kuma a halin yanzu an rasa yadda za a yi da su.