1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Ketare game da siyasar duniya.

Mohammad Nasiru AwalNovember 10, 2003
https://p.dw.com/p/BvqO
To batun matakan farfado da tattalin arzikin Jamus da halin da ake ciki a Iraqi na daga cikin muhimman batutuwan da jaridun ketare suka rubuta sharhi akai.

Da farko bari mu fara da sharhin da jaridar kasar NL Volkskrant ta rubuta dangane da takaddamar da ake yi tsakanin gwamnatin Jamus da ´yan adawa akan batun yiwa manufofin tattalin arziki kwaskwarima. Jaridar ta ce jam´iyar adawa ta CDU ba zata iya ci-gaba da yin karar tsaye don hana a aiwatar da shirin rage harajin ma´aikata ba. Jaridar ta yi nuni da wani binciken jin ra´ayin jama´a da aka gudanar, wanda ya bayyana cewa daukacin Jamusawa na goyon bayan shirin shugaban gwamnati Gerhard Schröder na yi musu sassaucin haraji. A saboda haka babu daya daga cikin bangarorin biyu da zai so ya rasa goyon bayan jama´a game da wannan batu mai sarkakiya.

Ita kuwa jaridar Der Standard ta birnin Vienna ta yi hange ne akan makomar siyasar tarayyar Jamus, tana mai cewa kawo yanzu shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya samu nasarar ceto gwamnatinsa ta hadin guiwa musamman dangane da matakan sauye-sauye da ake aiwatarwa a cikin kasar. To amma a badi ba haka zata kasance ba, musamman idan aka yi la´akari da zabuka 14 da zasu gudana a cikin jihohin kasar a shekara ta 2004. Jaridar ta ce yanzu haka dai ana iya yin hasashen cewar a badi jam´iyar SPD ba zata samu yadda take so ba. Domin hakan zai nuna ko Schröder zai cika wa´adin shugabancin sa zuwa shekara ta 2006.

Yanzu kuma sai yankin GTT, inda jaridar La Stampa ta kasar Italiya ta yi tsokaci akan halin rashin sanin tabbas da ake ciki a Iraqi. Jaridar ta ce a karshen makon da aka fuskanci hali na zub da jini mafi muni tun bayan faduwar birnin Bagadaza, yanzu dai ya tabbata cewa yawan rayukan da suka salwanta ya fi na zamanin yakin Gulf na farko. Jaridar ta ce sojojin Amirka da ake kashewa a kullu yaumin na kara yin barazana ga shugaba Bush. Haka zalika fatan da Bush ya ke na samun taimako daga kawayensa ya gamu da cikas, bayan da kasar Turkiya ta ce ba zata tura dakarunta zuwa Iraqi ba.

Ita kuwa jaridar Ricespospolita ta kasar Poland sharhi ta yi game da sojojin Poland din da aka tura Iraqi tana mai cewa an yi hakan ne saboda dalilai na siyasa, don nunawa Amirka zumunci, wanda Poland din ta yi mata alkawari tun bayan hare-haren 11 ga watan satumba. Yanzu kuma sai kasar Denmark inda jaridar Berlinkgske Tidende ta rubuta sharhi akan wani rohoto da hukumar kungiyar tarayyar Turai ta fitar game da shirye-shiryen da kasashen da za´a dauke su cikin kungiyar ke yi.

Jaridar ta rawaito rahoton hukumar ta EU wanda a ciki ta ce har yanzu kasar Poland da sauran sabbin kasashen da za´a dauke su cikin kungiyar EU a ran daya ga watan mayun shekara mai zuwa ba su kammala shirye-shiryen da suka wajaba don shiga cikin kungiyar ba. Jaridar ta ce hakan dai ba abin mamaki ba ne, domin sabbin kasashen sun ga cewa su kansu kasashen dake cikin kungiyar yanzu ba su mayar da hankali wajen cika ka´idojin kungiyar ta EU ba. To Allah Ya kyauta. Jama´a karshen sharhunan jaridun kasashen duniya kenan na wannan mako.