1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Zainab Mohammed Abubakar RGB
October 20, 2017

Jaridun Jamus a wannan makon sun yi nazari kan batutuwa da dama da suka auku a kasashen Afirka kama daga Najeriya kan batun batan jagoran fafutukar kafa kasar Biafra ya zuwa matsalar yunwa a Afirka.

https://p.dw.com/p/2mF1a
Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
Hoto: DW/K. Gänsler

Jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta yi tsokaci kan Tarayyar Najeriya a labarin da ta rubuta mai taken "Najeriya na wasa da wuta" jaridar ta ce jagoran fafutukar kafa kasar Biafra ya ranta a na kare ya bar baya da kura. A shekara ta 1967 yakin basasa ya barke a Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutane sama da miliyan guda. Mafi yawa sun mutu ne daga yunwa da cututtuka da suka kamu da su sakamakon barkewan yakin fafutukar neman 'yancin kan Biafra. A wancan lokaci an shaidar da ganin gawarwakin yara kanana a baje akan tituna. Shekaru 50 bayan wannan, fafutukar ballewar yankin na Biafra ya sake kunno kai. Jagoran fafutukar wanda ke zaman beli bisa zargin cin amanr kasa kuma ya kamata ya bayyana a kotu ranar Talata, Nnamdi Kanu ya yi batan dabo.Magoya bayanshi sun ce sojojin Najeriyar sun kasheshi, a yayin da gwamnati a hannu guda ta ce ya tsere ne tun bayan da sojojin suka afkawa gidansa. Rashin sanin inda Kanun ya ke ya tilasta kotu dage zaman shari'ar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba.

Hunger im Sahel Bildergalerie Tschad
Hoto: Andy Hall/Oxfam

Ita kuwa jaridar Die Welt nazari ta yi dangane da karuwar mutane da ke ci gaba da tagayyara sakamon yunwa, lamarin ya sa Majalisar Dinkin Duniya rage yawan abinci da take bai wa sansanonin 'yan gudun hijira, wanda ke nufin tarihi na neman maimaita kansa dangane da rikicin tururuwar 'yan gudun hijira da aka fuskanta a baya, jaridar ta ci gaba da cewar, a watanni kalilan kafin a samu kwararar 'yan gudun hijira daga Siriya da Jordan da Labanon da Turkiyya zuwa nahiyar Turai a shekara ta 2015, Majalisar ta rage yawan abincin da ake bai wa sansanonin 'yan gudun hijira bisa dalilai na rashin kudi. Rashin bada tallafi na kudi da kayayyakin da 'yan gudun hijirar ke bukata, na zama daya daga cikin manyan kura-kuran da aka yi dangane da manufofi na ketare a tarihin shekarun baya bayan nan. Wannan batu ya taso ne domin a yanzu haka tilas sai da hukumar bada tallafin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta rage yawan abinci da take bai wa sansanonin 'yan gudun hijra da ke Kenya da Yuganda. A kwai dubban 'yan gudun hijira daga kasar Sudan ta Kudu da sauran kasashen da ke makwabtaka da ke fama da rigingimu na yaki. Dalilin rage abincin kuwa shi ne, rashin isasshen kudi a bangaren Majalisar.

Mali Selbstmordanschlag in Gao
Hoto: Reuters

Daga batun yunwa a sansanin 'yan gudun hijira a Yuganda da Kenya sai kuma shirin samar da zaman lafiya a Mali. Inda jaridar Der Tagesspiegel ta rubuta wani sharhi mai taken "Da tsari irin na You Tube rundunar sojan Jamus ta koyi darasi " domin da na gaba ake sanin zurfin ruwa.Tun a ranar Litinin din nan, rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr ta wallafa sabon shirinta na daukar sojoji a karkashin taken "Mali". Rukunin farko na daukar sojojin a wasu lokuta ya fuskanci suka, duk da haka ta sake sabon yunkuri. A wannan karon shirin ya mayar da hankali kan balaguron wata takwas na jami'ian soji shida da mata biyu, da mai daukar hoto.Cikin makonni hudu masu karatowa ana sa ran kammala wasu kananan bidiyoyi guda 40 da za'a wallafa ta hanyoyin You Tube da sauran shafukan sada zumunta kamar Facebook da Twitter da Instagram, amma daga kasar Mali, inda rundunar ke aikin kiyaye zaman lafiya.