1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus akan nahiyar Afirka.

Mohammad Nasiru AwalDecember 3, 2004

A cikin wannan mako jaridun sun fi mayar da hankalin ne akan bikin ranar AIDS ta duniya, wadda aka yi a ran laraba da ta wuce da kuma yadda wannan cuta ke yaduwa kamar wutar daji a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/Bvpc

A cikin wani dogon sharhi da ta rubuta jaridar Tageszeitung (TAZ) ta fara ne da taken bikin ranar AIDS ta bana, wato Mata, ´yan mata, HIV da AIDS. Sannan sai ta ci-gaba da cewar daga cikin mutane miliyan 39.4 dake dauke da kwayoyin HIV a duniya, rabinsu mata ne. Jaridar ta rawaito rahoton cutar AIDS na shekara ta 2004, wanda ya nunar da cewa an fi fama da matsalar yaduwar kwayoyiin HIV a kasashen Afirka Kudu da Sahara, inda a nan ma mata ne suka fi kamuwa da kwayoyin cutar. Jaridar ta nunar da cewa managartan hanyoyin yaki da yaduwar wannan annoba sun hada da ba da ilimi mai nagarta, samarwa mutane aikin yi da kuma nuna adalci tsakanin jinsuna.

Ita kuwa a sharhin da ta rubuta jaridar Frankfurter Rundschau (FR) ta mayar da hankali ne akan namijin kokarin da tsohon shugaban ATK Nelson Mandela yake yi wajen jawo hankalin jama´a musamman a kasar ATK inda alkalumman lissafi suka tabbatar da cewa mutane miliyan 5.4 daga cikin al´umar kasar su miliyan 45 ke dauke da kwayoyin HIV. Mandela mai shekaru 86 da haihuwa, ya na shiga kowane lungu da sako na ATK don wayarwa da jama´a kai game da cutar AIDS. Yanzu haka dai kamar yadda jaridar ta rawaito, mista Mandela ya zama babban mai yaki da yaduwar cutar AIDS a ATK.

A farkon wannan mako aka fara wani taron kasashen duniya a birnin Nairobin Kenya, akan binnannun nakiyoyin karkashin kasa. A wani rahoto da ta buga dangane da wannan taro, jaridar Die Welt ta rawaito shugabannin kasashen Afirka na yin kira da kasashen Amirka da Rasha da kuma Sin da suwa Allah da Annabi su rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta haramta amfani da nakiyoyin karkashin kasa.

Ita ma jaridar TAZ ta yi tsokaci akan wannan taro, wanda ta ce shine irinsa na farko tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar birnin Ottawa shekaru biyar da suka wuce. Jaridar ta yi fatan cewa za´a cimma tudun dafawa bisa manufa, musamman bayan da a cikin wannan mako kasar Habasha ta shiga jerin kasashen duniya da suka albarkaci wannan yarjejeniya.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi ne game da zaben shugaban kasa da na ´yan majalisar dokokin Mozambik, inda ta ce bayan shekaru 18, an kawo karshen mulkin shugaba Joaquim Alberto Chissano. Zaben wanda ya gudana a ranakun laraba da alhamis, an yi takara ne tsakanin mutane 6, amma wadanda suka fi daukar hankali a ciki su ne sakatare janar na jam´iyar Frelimo Armando Guebuza da shugaban jam´iyar Renamo Afonso Dhilakama. Dukkan jam´iyun biyu sun samo asali ne daga tsofaffin kungiyoyin ´yan tawayen kasar.

Ita kuwa jaridar Die Welt cewa ta yi za´a samu sauyin mulki a kasar Mozambik. Jaridar ta ce yanzu haka dai birnin Maputo wato babban birnin kasar yana kyalli kamar jariri. A cikin shekaru 4 da suka wuce an bude sabbin kantuna da manyan otel-otel masu ban sha´awa da gidajen cin abinci a tsakiyar birni, to amma a wajen birni har yanzu tsofaffin gidajen laka ne suka fi yawa. Kana kuma babu wutar lantarki da tsabtattacen ruwan sha. Jaridar ta kammala wannan rahoton da cewar duk da wannan bambamci na ci-gaba wanda kasar ta gada bayan ta yi fama da yakin basasa na tsawon shekaru 16 da kuma matsalolin talauci da na cin hanci da karbar rashawa, Mozambik na matsayin zakaran gwajin dafi musamman wajen shimfida sahihin mulkin demukiradiyya a nahiyar Afirka.