1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka a makon (9 zuwa 13.08.04)

Mohammad Nasiru AwalAugust 13, 2004
https://p.dw.com/p/Bvpn

Jama´a barkanku da warhaka. A wannan makon ma jaridun na Jamus sun fi tabo rikicin yankin Darfur dake yammacin kasar Sudan. A cikin wani rahoto da sanyawa taken ana ci-gaba da tashe-tashe hankula a Darfur jaridar Tageszeitung cewa ta yi har yanzu ba ta canza zani ba dangane da tsaro da mawuyacin halin da dubun dubatan mutane ke ciki a Darfur duk da alkawuran da gwamnatin Sudan ta dauka na daukar sahihan matakan kawo karshen wannan rikici. Jaridar ta rawaito wani rahoto da kungiyar kare hakin dan Adam ta Human Rights Watch ta bayar a tsakiyar wannan mako, inda ta yi nuni da cewa a kullum ana kaiwa fararen halu hari tare da yiwa mata fyade. A saboda haka ba za´a iya daukar alkwarin da gwamnatin Sudan ta yi na kare al´umar wannan yanki daga ta´asar sojojin sa kai larabawa da muhimmanci ba. Kungiyar ta HRW ta ce girke karin dakarun kungiyar tarayyar Afirke ne kadai zai taimaka a samu saukin wannan halin da ake ciki, to amma ba wanda ya san ranar da za´a yi haka domin kungiyar ta AU ta dakatar da zaman taron da take yi da nufin tattauna batun tura karin dakaru zuwa Darfur, har sai abin da hali yayi. A wani rahoton kuma jaridar ta TAZ ta labarto mana cewa dukkan kungiyoyin ´yan tawayen Darfur sun amince hukumar samar da abinci ta MDD ta kai kayan agaji zuwa yankunan da ke hannun ´yan tawaye.

Ita kuma jaridar Frankfurter Rundschau cewa ta yi an kame mutane da dama a yankin Darfur bisa zargin cewa sun yi hira da ´yan kasashen waje a dangane da mawuyacin hali da ake ciki a wannan yanki.

Ita kuwa a sharhin da ta rubuta jaridar Frankfurter Allg. Zeitung ta yi tsokaci game da matsalar farin dango da ta addabi wasu kasashen yammacin Afirka guda 6 musamman ma kasar Mauritania. Jaridar ta ce ya zuwa yanzu farin dango sun lalata gonaki da girmar su ya kai hektar miliyan daya. Yanzu haka dai farin dangon sun warwatsu zuwa kasashen tsakiya da gabashin Afirka. Abin damuwa shine ba wani maganin kashe kwari maras illa ga muhalli da za´a iya amfani da shi akansu. Jaridar ta kara da cewa hasashen ne kadai za´a iya yi game da barnar da farin dango zasu yi, domin a lokacin da aka fuskanci irin wannan matsala a Sudan a cikin shekarar 1987 sai da aka kwashe shekaru biyu kafin a shawo kan wannan matsala, bayan sun mamaye kasashe 28. Ita ma a sharhin da ta yi game da wannan annoba jaridar TAZ ta rawaito kungiyar abinci da aikin gona ta MDD wato FAO na yin kira ga kasashen duniya da su kara matsa kaimi wajen yakar farin dango. Yanzu haka dai ana bukatar kudi kimanin dalar Amirka miliyan 80 a cikin watanni biyu don hana yaduwar farin dango, amma kawo yanzu dala miliyan 10 kadai aka samu. Jaridar ta ce ana bukatar sahihan matakan yaki da wannan annobar, idan ba haka kuwa to mutane kimanin miliyan daya a wata kasa dake cikin jerin kasashe da suka talauci a duniya, zasu fuskanci barazana ta matsananciyar yunwa.

Yanzu kuma sai Liberia inda a wannan makon aka yi bikin shekara daya da kifar da gwamnatin tsohon shugaba Charles Taylor. A cikin wani sharhi da ta rubuta jaridar TAZ ta ce watanni 12 bayan an tilastawa Charles Taylor yin kaura zuwa tarayyar Nijeriya, yanzu dukkan makamai da tankokin yaki sun bace daga birnin Monrovia, kana kuma mazauna wannan birni na gudanar harkokinsu ba tare da wata fargaba ba. To sai dai ana zargin sabuwar gwamnatin wucin gadin kasar da aikata zamba. To Allah Ya kyauta. Jama´a yau kuma a nan zamu dakata sai mako na gaba in Allah Ya kaimu.