1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridu akan Al'amuran Afirka

July 10, 2009

Taron Ƙasashe masu cigaban masana'antu ya duba halin da ake ciki a Afirka

https://p.dw.com/p/Il3n
Zauren taron G8 a L'AquilaHoto: AP

Taron ƙolin ƙasashen G8 da suka fi ci gaban masana'antu a duniya da kuma dangantakarsu da Afurka shi ne muhimmin abin da jaridun Jamus suka fi mayar da hankali kansa dangane da rahotannin da suka bayar a game da nahiyar ta Afurka. Jaridar Süddeutsche Zeitung, a cikin nata rahoton cewa tayi:

"Shawarar da ƙasashe masu ci gaban masana'antu na G8 suka zayyana a game da tinkarar matsalar yunwa a nahiyar Afurka, tana fuskantar kakkausan suka daga ɓangarori da dama. Domin kuwa kawo yanzu ba su cika alƙawururrukan da suka sha gabatarwa a tarukan ƙolinsu na baya ba duk kuwa da raɗaɗin da ƙasashe masu tasowa na Afurka ke fama da shi sakamakon matsalar tattalin arziƙin duniya, wadda su kansu kasashe masu wadatar masana'antu na G8 ne ummal'aba'isinta."

Ita kuwa jaridar Financial Times Deutschland cewa tayi:

Nicolas Sarkozy mit Abdoulaye Wade
Abdoulaye Wade na Senegal da Nicholas Sarkozy na FaransaHoto: picture-alliance/dpa

"Nahiyar Afurka ta fi kowane ɓangare na duniyar nan fama da raɗaɗin rikicin kuɗi da gurɓacewar yanayi, lamarin da ya sake mayar da hannun agogo baya a fafutukar raya makomar nahiyar. Duk wata tafiyar hawainiyar da za a samu dangane da bunƙasar tattalin arziki ta kan yi tasiri kai tsaye a harkokin rayuwa ta yau da kullum, kama daga abinci da kiwon lafiya da ilimi. Hakan na mai ma'ana ne cewar za a sake komawa gidan jiya, abin da zai ƙara haifar da tazara a ƙoƙarin jumma burin nan na shekarun dubu biyu."

A ƙasar Liberiya, a wannan makon hukumar tantance gaskiya a game da yaƙin basasar ƙasar ta ba da shawarar kakkaɓe shugaba Ellen Johnson Sirleaf daga kan muƙaminta, amma ba tare da ta ba da dalili ba. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Ainihin abin dake akwai, lamarin da kuma ita hukumar ba ta ambata ba a cikin rahotonta shi ne zargin da ake yi na cewar shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta ba wa ƙungiyar National Patriotic Front ta tsofon shugaba kuma madugun 'yan tawayen Liberiya goyan baya. To sai dai kuma su kansu wakilan hukumar ta tsage gaskiya, babu ɗaya daga cikinsu da ya tsira daga irin wannan zargi na bai wa ɗaya daga cikin sassan Liberiya da basa ga maciji da juna a lokacin yaƙin basasar ƙasar. Abin fata dai shi ne kada wannan taƙaddama ta zama cikas ga ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiyar Liberiya."

Ellen Johnson Sirleaf
shugabar Liberia Ellen Johnson SirleafHoto: picture-alliance/dpa

Ƙasashen Afurka sun samu kyakkyawan ci gaba a fannin yaɗa labarai da 'yancin 'yan jarida da faɗin albarkacin baki, to sai dai kuma a faɗin jaridar GIGA Focus Afrika, sakamakon wani nazarin da aka yi ya nuna cewar ba tabbas a game da ainihin masu mallakar kafofin yaɗa labaran, ballantana a yi batu game da maƙasudinsu ko kuma alƙiblar da suka fuskanta. Domin kuwa galibi zaka tarar ko da wasu hamshaƙan 'yan kasuwa ne ko kuma tsaffin soja da suka yi mulki su ne ke mallakar kafofin yaɗa labaran.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Mohammed