1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karsai Afghanistan

September 17, 2009

A sakamakon zaɓen Afghanistan, hukumar zaɓe ta ce Karzai ya samu nasara

https://p.dw.com/p/JitB
Hamid KarzaiHoto: Picture-alliance/dpa

Hukumar zaɓe ta ƙasar ta ce a halin da ake ciki yanzun dai shugaba Hamid Karzai shi ne ya lashe zaɓen ƙasar. In har hakan ta tabbata, duk da ƙorafin maguɗin da ake yi, ke nan za a ci gaba da tafiyar da manufofin da kawo yanzu ba su haifar da wani ɗan mai ido ga ƙasar Afghanistan ba.

A dai halin da ake ciki yanzu ba tabbas a game da ko cewar sakamakon da hukumar zaɓen ta bayar zai saura akan haka. Tilas a jira a ga irin martanin da hukumar ɗaukaka ƙara, wadda MƊD ke da hannu a cikinta, zata mayar dangane da zargin maguɗin zaɓe da tawagar sa ido ta ƙungiyar tarayyar Turai ta yi. Idan har ta nuna rashin ingancin da yawa daga cikin ƙuri'un da aka kaɗa ta yadda zai zama tilas a shiga wani zaɓe na fid da gwani, ba shakka al'amura zasu canza su ɗauki wani sabon salo.

Amma kuma ko da a ce ba a samu wani canji ba, al'amura suka ci gaba da kasancewa kamar yadda hukumar zaɓen ta sanar, wa'adi na biyu na mulkin shugaba Karzai zai kasance tattare da tabo. Ba kuma maguɗin zaɓe ne kaɗai dalilin haka ba, wanda shi ma abokin adawarsa Abudullah ke da rabonsa na alhaki, sai dai saboda rashin taɓuka wani abin a zo a gani a wa'adin mulkinsa na farko.

Gwamnatin Karzai, wadda aka saka dogon buri game da ita ta sanya murna ta koma ciki. A cikin jerin lissafin ƙasashen da suka ci tura game da manufofinsu ƙasar Afghanistan ta zama cikon ta takwas a shekara ta 2006 a yayinda a shekarar da ta wuce ta ƙara samun koma baya inda ta zo cikon na shida. A ɗaya ɓangaren kuma ƙasar sai daɗa durmuya take cikin matsalar talauci, inda kimanin kashi 40 cikin ɗari na al'umar Afghanistan ke zama hannu baka hannu ƙwarya.

Koma bayan tattalin arziƙin da taɓarɓarewar al'amuran tsaro ba sun zo ne a ba zata ba. Bisa akasin haka ma manufofin Karzai su ne umma'aba'isin haka. Domin kuwa tun da farkon fari Karzai bai ba da la'akari da buƙatun jama'a bayan kawo ƙarshen yaƙin basasa da kutsen soja da aka yi ƙasar. Abin da ya fi ba wa fifiko shi ne ƙarfafa ikonsa, inda ya shiga ƙulla yarjeniyoyi da masu zazzafar aƙida da haulaƙan yaƙin ƙasar da kuma wasu 'yan kasuwa masu neman arzuta kansu ko ta halin ƙaƙa. Muhimmin abin da Afghanistan ke buƙata a yanzun shi ne wasu nagartattun manufofin da zasu tabbatar da tsaro a ƙasar a ƙarƙashin yanayi na demoƙraɗiyya tsantsa.

Mawallafi: Tijani Lawal

Edita: Zainab Mohammed