1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi kan yaki da ta'addanci a yankin Sahel

Mohammad Nasiru Awal RGB
December 15, 2017

Alkawarin da kasashen Jamus da Faransa suka dauka na taimakon kasashen kungiyar G5 Sahel a yaki da ta'addanci na daga cikin muhimman batutuwan nahiyarmu ta Afirka da suka dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

https://p.dw.com/p/2pR8o
Frankreich Treffen Staatschefs - Kampf gegen IS in der Sahelzone in Afrika
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Euler

A labarin da ta buga mai taken samar da rundunar soji ga kasashen Sahel jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi- a yakin da ake yi da kungiyoyin tarzoma a Afirka, Jamus da Faransa sun fuskancin alkibla guda, inda daga yanzu maimakon su tura sojojinsu, sun kuduri aniyar ba da gagarumin taimako ga kasashe biyar na G5 Sahel da suka hada da Mali da Burkina Faso da Mauretaniya da Nijar da kuma Chadi ta yadda su da kansu za su kafa rundunar da za ta jagoranci yaki da ta'addanci a wannan yanki, wanda acewar jaridar, kungiyoyin Jihadi da dama sun samu gindin zama a ciki. Jaridar ta ce ba ya ga taimakon sojoji, habaka ayyukan raya kasa da ci gaban al'umma za su taka muhimmiyar rawa don cimma manufar da aka sa gaba.

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da Adama Barrow na Gambiya
Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da Adama Barrow na GambiyaHoto: picture alliance/dpa/B. v. Jutrczenka

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci a kan batun na yaki da ta'addanci a yankin Sahel tana mai cewa tafiyar hawainiya wajen hada kan rundunar kasashen Afirka don yaki da 'yan ta'adda. Ta ce shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar a gaban wani taron koli cewa kasar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa za su tallafa wa kasashen yankin Sahel da makudan kudade a yaki da ta'adda. To amma hakan ba ya nufin maye gurbin sojojin Faransar. Jaridar ta ce har yanzu dai Faransa wadda a farkon shekarar 2013 karkashin Shubaba Francois Hollande ta tura sojoji Mali don fatattakar masu Jihadi, yanzu haka tana nazarin dubarun janye sojojinta.

Mali Gao Operation Barkhane Kinder und französische Soldaten
Yara a tare da sojojin Faransa a MaliHoto: Getty Images/AFP/P. Desmazes

Ziyarar da shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya kai wannan mako a kasashen Ghana da Gambiya ita ce ta dauki hankalin jaridar Süddeutsche Zeitung inda ta fara da tambayar shin me Jamus za ta koya daga Ghana? Jaridar da kanta ta ba da misali da cewa yadda za a kafa gwamnati mai karfi. Ta ce ziyarar ta kwanaki hudu a kasashen na Ghana da Gambiya za ta ba wa Steinmeier sararawa daga dambarwar siyasa a gida inda har yanzu ake kokarin kafa gwamnati tun bayan zaben majalisar dokoki a cikin watan Satumba. Ghana na zama abin koyi ga sauran kasashen Afirka musamman a tsarin demokradiyya da kwanciyar hankali, shi yasa Jamus ke kokarin inganta huldodi a fannoni dabam-dabam da kasar ta Ghana. Bari mu kammala da jaridar Berliner Zeitung wadda ta buga labari game da sabuwar dangantaka tsakanin Rasha da Sudan.Ta ce bayan da Rasha ta sanar da kawo karshen aikin sojinta a Siriya, yanzu fadar Kremlin ta fara kulla wata huldar aikin soji da kasar Sudan, inda tuni ma rahotannin suka ce jami'an sojin Rasha su fara ba wa dakarun Sudan horo.