1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Dabarun neman sauya gwamnati a Iran

von Hein Matthias Kommentarbild App
Matthias von Hein
May 23, 2018

Bayan da Amirka ta sanar cewa za a kakaba wa Iran takunkumai mafi tsauri a tarihi, take-taken gwamnatin Amirka karkashin jagorancin Donald Trump shi ne a samu sauyin gwamnati a kasar inji Matthias von Hein.

https://p.dw.com/p/2yC6z
Mike Pompeo US Außenminister
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. S. Applewhite

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya sanar cewa za a kakaba wa Iran takunkumai mafi tsauri a tarihi. Sai dai take-taken gwamnatin Amirka karkashin jagorancin Donald Trump ba saboda tsaron Amirkar ba ne, buri shi ne a samu sauyin gwamnati a Iran, inji Matthias von Hein na tashar DW a cikin wannan sharhi.

Mike Pompeo ya zabi wuri mafi dacewa don yin jawabinsa na farko mafi girma kan manufofin ketare. A shekaru uku da suka wuce me sabon sakataren harkokin wajen na Amirka ya bayyana matsayinsa ka yarjejeniyar nukiliar Iran a gaban gidauniyar Heritage Foundation ta masu ra'ayin rikau.

Matthias von Hein
Matthias von Hein na DWHoto: DW/M. von Hein

A jawabinsa na ranar Litinin ma ya tabo batun amma a wannan karo bisa karfin ma'aikatarsa da goyon baya daga shugaban kasa. Dole ne a soki lamirin Iran dangane da abubuwan da take yi a yankin Gabas ta Tsakiya da ma yadda gwamnatin kasar ke gudana. Amma yin gaban kai da Pompeo ya yi a jawabin ya sanya shakku a ciki.

Gabatar da wasu batutuwa zababbu da yadda aka juya gaskiya ko ma watsi da ita ya sanya ayar tambaya ko za a samu wani ginshiki ba bai daya don tattaunawa tsakanin Turai da Amirka a kan batun na Iran. 

Kalaman da ke fitowa daga Washington shi ne Amirka na son ta jagoranci wata tattaunawa, amma a gaskiya Pompeo da gwamnatin Trump ba su da alamar shiga wata tattaunawa, hasali ma matsin lamba suke na a yi aiki da ra'ayinsu ko an ki ko an so. Sharudda 12 da Pompeo ya gindaya wa gwamnatin Iran wani mataki ne na neman durkusar da tattalin arzikin kasar Iran din.