1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Barazanar sauyin yanayi a Afirka

Deutschland Eco Hero Yahaya Ahmed Becker
Yahaya Ahmed
November 15, 2017

A sharhin da ya rubuta yayin da ake gudanar da taron duniya kan sauyin yanayi a Jamus, Mal. Yahaya kwararre kan muhalli da ke jihar Kaduna ya ce Najeriya na cikin kasashen duniya da sauyin yanayi ya yi wa illa.

https://p.dw.com/p/2ng2g
Deutschland Eco Hero Yahaya Ahmed Becker
Hoto: DW/T. Walker

Shekaru 40 da suka gabata ruwan tafkin Cadi gaba dayansa, ya mamaye haraba ne wanda girmanta ya kai murabba'in kilomita dubu 40. A yanzu kuwa saboda canje canjin yanayin da aka samu, harabar da tafkin ya ƙunsa gaba daya, bai fi murabba'in kilomita dubu daya da 300 ba sakamakon aukuwar fari da shanyewar ruwan tafkin, abin da ke alakanta shi da ƌumamar yanayi.

Afrika - Tschadsee
Hoto: Getty Images/AFP/S. K. Kambou

A yankin Guinea Savannah kuma, an lura cewa dazuzzukan da ke yankin yanan ci gaba da raguwa saboda yawan sare bishiyoyi da ake ta yi don samar da makamashi, wato itacen girki. Hakan kuwa na daya daga cikin dalilan da ke ƙara hanzarta kwararowar hamada da ake samu a yankin a kowace shekara. Idan kuma aka waiwaya a kudu maso gabashin Najeriya, nan ma za a ga cewa, zaizayar ƙasa ne ke ƙalubalantar mazauna wannan yankin, inda sakamakon haka dimbin yawan mutane ke asarar kadarorinsu, abinda ke haddasa ƙangin talauci.

Nigeria Spannungen im Niger Delta
Hoto: DW/B. Muhammad

Ambaliyar ruwa kuma, ita ce matsalar da ke ƙalubalantar muhalli da mazauna yankunan gaƃar teku a duk fadin Kasar. Alal misali, duk da arzikin man fetur da yankin Naija Delta ke alfahari da shi, hakan bai ceto yankin daga barazanar mamayar da ambaliyar ruwa ke yi masa a ko wace shekara ba. A nan dai, abin tambaya shi ne, wane irin nauyi ya rataya a wuyar nahiyar Afirka da kuma Najeriya game da daukan matakan magance barazanar da sauyin yanayi ke yi.?

A nawa ganin dai, farkon abin yi a nan, shi ne yawaita da kuma inganta shirye-shiryen fadakar da jama'a na ko wane nau'i don fahimtad da su da kuma ilimintad da su game da ire-iren ababan da ke wakana. A nan kuwa, zai fi dacewa ne a sami hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi, da kafofin yada labarai, da cibiyoyin cinikayya da masana'antu wajen aiwatar da shirye-shiryen. Wajibi ne a kafa cibiyoyin ƙarawa juna ilimi, inda za a horas da jami'an shiyyoyin da aka ambata don su faƌakar da sauran jama'a.

Bangladesch Erneuebare Energie
Hoto: DW/M. Mostafigur Rahman

A halin da ake ciki yanzu, a yankin nahiyar Afirka kudu da Sahara musamman a Najeriya, ana samar da fiye da rabin makamashin da ake amfani da shi ne ta hanyar Janareto da kuma man fetur ko gas. To a maimakon haka, don rage fitar da hayaƙin da ke janyo dumamar yanayi da gurbata yanayi, za a iya kakkafa allunan nan na Sola a kan rufin gidaje don samar da makamashin wutar lantarki mai tsabta. Za a iya ƙara yin amfani da hayaƙin gas wanda aka fi sani da suna LPG wanda a halin yanzu ake ta ƙona mafi yawansa a banza dare da rana a Najeriya, ko kuma hayaƙin Biogas wanda ake samarwa daga sharan noma da na sauran gurƃatattun kayayyakin abinci.

Ba a kan gwamnati kawai, ya kamata a ƌora wannan nauyin ba. Sauran masana'antu da cibiyoyin kasuwanci, da kafofin yada labarai, da sassa daban-daban na hukumomi da na masu zaman kansu, na da rawar takawa don a cim ma wanna burin.