Sharhi akan Wasannin Olympics | Siyasa | DW | 30.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi akan Wasannin Olympics

A jiya lahadi ne aka gabatar da shagulgulan rufe wasannin Olympics, wadanda aka yi tsawon kwanaki 17 ana gudanar da su a birnin Athens, fadar mulkin kasar Girka

Shagulgulan rufe wasannin Olympics a Athens

Shagulgulan rufe wasannin Olympics a Athens

Duk da cewar wasannin da aka yi tsawon kwanaki 17 ana gudanarwa a Athens ta kasar Girka sun kasance masu burgewa matuka ainun, inda bayanai suka nuna samun karin kashi 20% na yawan mutannen da suka kalli wasannin ta akwatunan tekebijin a sassa dabam-dabam na duniya, idan an kwatanta da zamanin baya, amma a daya bangaren mutane sun yi hamdalla da ganin wasannin sun zo karshensu ba tare da fuskantar tashe-tashen hankula ba. Daga cikin abubuwan da suka taka muhimmiyar rawa wajen kwantar da kurar rikici a birnin na Athens shi ne halin sanin ya kamata da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya nunar na amincewa da kin halartar shagulgulan rufe wasannin a jiya lahadi. Kuma ko da yake matasa da suka shiga wasannin na Olympics sun samu ikon gudanar da bukukuwa na nishadi iri dabam-dabam a tsawon kwanaki 17 aka yi ana gudanar da wasannin, amma tsauraran matakai na tsaro da aka dauka domin kandagarkin ayyukan tarzoma, sun gurbata yanayin lamarin baki daya. Daukar wadannan matakai abu ne da ba makawa game da shi nan gaba, ba ma a wasannin Olympics kadai ba har da sauran wasanni na kasa da kasa, kamar gasar cin kofin kwallon kafa na duniya. Wani abin madalla kuma shi ne kasancewar ba a fuskanci yamutsi kamar yadda aka yi hasashe da farko ba. Domin kuwa makonni kalilan kafin a cunna wutar wasannin na Olympics, kusan ba wanda yayi zaton cewar al’amura zasu tafi salin-alin ba tare da an fuskanci tangarda ga tsare-tsaren wasannain ba. Amma a karshe dukkan ‚yan wasa da kafofin yada labarai sun yaba da filaye da kuma kafofin da aka gudanar da wasannin a cikinsu. Hatta ire-iren yamutsinnan na cunkoson motoci a tituna bai samu ba sakamakon sabbin hanyoyin jiragen karkashin kasa da aka gina domin samun saukin jigilar dubban dauruwan mutanen da suka tsunduma zuwa birnin Athens domin shaidar da wasannin. Ba shakka birnin zai rabanta da wadannan sabbin hanyoyi nan gaba. Masu alhakin shirya wasannin a kasar Girka sun cika alkawarin da suka yi tun da farkon fari na cewar wasannin Olympics sun dawo gida, inda aka lura da haka a shagulgulan bude wasannin dake da tarihin sama da shekaru dubu uku a wannan kasa. To sai dai kuma murnar Girkawan ta koma ciki a game da fatan da suka yi na dawo da wasannin baki daya zuwa kasar tasu sakamakon tabargazar da ‚yan wasannin motsa jiki na kasar suka caba. ‚Yan wasan sun yi kunnen-uwar shegu da gargadin da shugaban kwamitin Olympics na duniya Jacques Rogge ya gabatar a jawabinsa na bude wasannin inda ya ce za a dauki tsauraran matakai, ba sani ba sabo, domin ladabtar da duk wani dan wasan da aka same shi da laifin amfani da magungunan kara kuzarin da aka haramta aiwatar da su. Amma wannan tabargaza ta shafa wa Girkawan kashin kaza. Kuma ko da yake ba za a komar da wasannin gaba daya zuwa kasar Girka ba, amma a daya bangaren da wasannin na bana da aka gudanar a birnin Athens ba. Wasanni na gaba nan da shekaru hudu masu zuwa za a gudanar dasu ne a Beijing ta kasar China, wacce tayi ta biyu a yawan lambobin da ‚yan wasanta suka lashe a baya ga ‚yan wasan kasar Amurka.