1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi Akan Taron Kolin Afurka

July 9, 2004

A taron kolinsu na yini uku a Addis Ababa shuagabannin Afurka sun bayyana cikakken shirinsu na tinkarar matsalolin dake addabar nahiyar

https://p.dw.com/p/BviG

Afurka tayi azamar tsame kanta da kanta daga mawuyacin hali na kaka-nika-yi da take ciki. Sakamakon taron koli na yini uku da shuagabannin kasashen suka gudanar a Addis Ababa ya bayyanar a fili cewar kasashen sun fuskanci wata sabuwar alkibla wajen neman hanyoyin magance rikice-rikicen nahiyar ba tare da dogaro akan taimako daga ketare ba. Mai yiwuwa manazarta daga kasashen Turai su kasance suna tattare da wani ra’ayi dabam game da sakamakon taron kolin, inda zasu yi korafin cewar maganganu ne da fatar baki da aka saba ji a zamanin baya. Masu irin wannan korafi sun fi kaunar ganin nahiyar Afurka ta dogara akan taimako daga ketare da kuma yin koyi da manufofin kungiyar tarayyar Turai. Amma duk wanda yayi bitar tarihi zai ga babu wata nasara da aka cimma a manufofi iri dabam-dabam da aka saba gabatarwa ga kasashen Afurka daga ketare, saboda wadannan manufofi ba su da wata nasaba da al’adu da tsare-tsaren zamantakewar al’umar Afurka. Kuma masu iya magana su kan ce: "Kayan aro ba ya ado." Duk wata gamayyar da bata da madogara bata da wata tsayayyar alkibla ta siyasa ko wata manufa da ta sa a gaba to kuwa ko shakka babu ba zata yi karko ba. Abu daya da zai iya hana ruwa gudu a game da kyawawan manufofin da aka tanadar a Addis Ababa shi ne matsalar rashin kudi. A wannan bangaren wajibi ne kafofi na kasa da kasa su ba da hadin kai ta yadda lamarin zai zama mai tasiri ga kowa-da-kowa. Dukkan jami’an siyasar da suka halarci taron na Addis Ababa sun bayyanar a fili cewar ba su da niyyar ci gaba da kasancewa ‚yan rakiya, musamman akan al’amuran da suka shafi makomar nahiyar Afurka. Taimakon kai da kai shi ne kawai zai taimaka wajen hana nahiyar Afurka ci gaba da dogaro akan kasashen ketare. Mahalarta taron na Addis Ababa sun fito fili suka bayyana kyamar shisshigi, walau daga kasashen yammaci masu ci gaban masana’antu ko kasar Libiya. Kasashen gaba daya sun bayyana shirin tinkarar matsalolin dake akwai ba kawai ta hanyar shawarwari ba kazalika har da katsalandan soja idan zarafi ya kama. Rikice-rikicen da ake fama da su a kasashen Sudan da Cote d’Ivoire da janhuriyxar Demokradiyyar Kongo duk sun taimaka wajaen ta da zaune tsaye a yankunan wadannan kasashe da kuma neman kai makobtansu su baro. Wadannan rikice-rikice na daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu wajen farfado da tattalin arzikin Afurka da kuma zuba jarin ‚yan kasuwa na ketare a wannan nahiya. Har yau sai lalube ake ci gaba da yi a cikin dufu wajen neman bakin zaren warware wadannan matsaloli ba tare da nasara ba, saboda dukkan sassan da lamarin ya shafa su kan sa kafa su yi fatali da yarjeniyoyin tsagaita wuta da na zaman lafiyar da aka cimma. Wani abin da zai nuna cikakken shiri da azamar shuagabyannin na Afurka game da canza wa manufofinsu alkibla kuma shi ne matakai da zasu dauka a cikin gida domin yaki da cin hanci da almubazzaranci da kuma bin safifin mulki na demokradiyya. A nasu bangaren kasashe masu ci gaban masana’antu na nahiyar Turai suna iya ba da tasu gudummawar ta hanyar kamanta adalci a dangantakarsu ta ciniki da ma’amallarsu ta siyasa da kasashen Afurka.