1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shakka babu Amirka na tafiyar da kurkuku na sirri a Turai, inji Marty

Wani dan majalisar dattijan kasar Switzerland dake binciken zargin da aka yi cewa hukumar leken asirin Amirka CIA na tafiyar da wasu gidajen kurkuku na sirri a Turai, ya ce tabbas Amirka ta gudanar da wasu ayyukan haramu a jigila da kuma tsare firsinoni. Dick Marty ya ce manufofin Amirka akan yaki da ta´adda sun sabawa dokokin kasa da kasa da suka shafi kare hakkin dan Adam. Mista Marty ya zargi wasu kasashen Turai da goyawa Amirka baya a wannan keta dokar da ta yi. Marty dai shi ke shugabantar wannan bincike a madadin majalisar kasashen Turai. Amirka dai ba ta amsa ba kuma ba ta musanta cewar tana tafiyar da gidajen sarka na boye a Turai ba.