Shaidun Kotu sunce Musawi ya cancanci hukuncin kisa | Labarai | DW | 04.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shaidun Kotu sunce Musawi ya cancanci hukuncin kisa

Shaidun kotu a kasar amurka sun yanke cewa Zakariya Musawi,da ake tuhuma da laifin harin ranar 11 ga watan satumba a Amurka,ya cancanci hukuncin kisa,saboda laifin kin sanarda hukuma shirin kai wannan hari kamar yadda ya amsa laifin nasa,inda yace yana sane da shirin kai harin na 11 ga watan satumba,lokacinda aka tsare shi wata guda kafin akai wannan hari.

A ranar alhamis ake sa ran yanke hukunci akan Musawi,mutum guda da ake tuhuma da alaka da harin na Amurka da yayi sanadiyar rayukan mutane kusan 3,000