1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi bikin sallah a Jamhuriyar Nijar

Tila Amadou
June 14, 2018

Al'ummar Musulmi a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da bikin Sallah Karama a wannan Alhamis bayan kammala azumin watan Ramadana, ko da yake al'umma na yin kukan matsin tattalin arziki da ya hana su samun abubuwan hidima.

https://p.dw.com/p/2za4B
Eid Al Fitr in Zinder, Niger
Hoto: DW/L. Malam Hami

Al'ummar jihar Agadez kamar sauran jihohi a Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da bikin Sallah karama. Tun da sanyin safiya jama'a suka shirya domin zuwa Sallar Idi. Mai martaba sarkin Abzin Elhadji Oumaru Ibrahim Oumaru bayan sakonsa na barka da sallah zuwa ga al'ummar Agadez, ya yi fatan zaman lafiya ga kasa baki daya. 

Batun koma bayan tattalin arziki a jihar Agadez bayan rufe wurin tonon zinariya mafi girma a jihar da gwamnatin Nijar ta yi da ma takaddama kan sana'ar safarar bakin haure sun kawo matsaloli masu yawa ga wasu iyalai da suka gagara samun kudin shiga don biyan wasu bukatu na su. Amman duk da haka wasu daga cikin al'ummar jihar ta Agadez sun baiyana farin cikinsu da ganin wannan rana bayan da suka kammala azumin na watan Ramadana lafiya.