Shagulggullan karamar salla a kasashen musulmi na dunia. | Labarai | DW | 03.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shagulggullan karamar salla a kasashen musulmi na dunia.

Bayan wata guda na ibadar azumin Ramadan yau ne a kasashe da dama, musulmi ke shagulgullan salla karama.

A mafi yawan kasashen Larabawa, da wasu kasashen musulmi na Afrika, da su ka hada da Gambia, Senegal, Guinee da dai sauran su an yi sallar idi a sahiyar yau cikin nishadi da farin ciki.

A wasu kasashen kuma kamar su Taraya Nigeria Jamhuriya Niger Mali da Libia, tun jiya a ka yi salar ta idi, a na kuma ci gaba da shagulugulla a yanzu haka.