1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Shirin sauya kudin zabe

Salissou Boukari
April 19, 2018

'Yan sanda a birnin Dakar na Senegal sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa wata zanga-zangar nuna adawa da sauya kundin zaben kasar da ke zuwa kasa da shekara daya kafin zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/2wKlj
Proteste gegen die Regierung in Dakar, Senegal
'Yan sanda sun saka hayaki mai sa kwalla wa masu zanga-zanga a Dakar kasar SenegalHoto: AP

'Yan sandan sun aiwatar da kame-kamen 'yan adawan cikinsu har da tsohon firaministan kasar Idrissa Seck da Malick Gakou wani kusa a bangaran 'yan adawan sannan da shugaban jam'iyyar Mouvement Agir Thierno Bocoum kaman yadda jam'iyyunsu suka tabbatar. Shi dai tsohon firamonistan kasar ta Senegal Idrissa Seck ya jagoranci gwamnatin kasar ne daga 2002 zuwa 2004 a karkashin jagorancin Shugaba na wancan lokacin Abdoulaye Wade. Masu zanga-zangar dai sun kafa shingaye a tsakiyar wani titi da ke zuwa majalisar dokokin kasar inda za a tattauna batun sauya kundin tsarin zaben.