Segolene Royal ′yar takarar shugaban kasar Faransa | Siyasa | DW | 18.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Segolene Royal 'yar takarar shugaban kasar Faransa

Segolene Royal na daya daga cikin 'yan takarar neman mukamin shugaban kasar faransa da zasu taka muhimmiyar rawa a zaben lahadi mai zuwa

Segolene Royal

Segolene Royal

Segolene Royal mace ce mai fara’a matuka gaya. To sai dai kuma a yanzun bata da cikakken kuzari bisa sabanin yadda ta kasance a zamanin baya sakamakon wahalar yakin neman zabe da kuma masu fuskantarta da tambayar cewa, wai shin wa zai kula da renon ‘ya’yanta in ta zama shugabar kasa? Segolene Royal ta ce ba a mata sassauci a yakinta na neman zabe kuma tana sauraron abubuwa na mamaki kafin zaben. Jami’ar siyasar mai shekaru 53 da haifuwa tana bin manufofi ne na kusantar jama’a, lamarin da ta kira wai ba wa jama’a cikakkiyar damar shiga a rika damawa da su daidai da manufar mulkin demokradiyya. Kowa na da damar tofa albarkacin bakinsa da ba da shawarwari bisa manufa. Segolene Royal ta ce:

“Faransawa mutane ne dake da cikakkiyar hazaka. Sun ankara da cewar abubuwa ba sa tafiya daidai yadda ya kamata a kasar. A saboda haka nike neman hadin kansu domin kyautata makomarta. Ra’ayoyinsu a gare ni daidai yake da ginshikin da ake bukata ga kowane gida”.

Ba tare da son mahaifinta ba, Segolene Royal ta halarci sakandare ta kuma shiga kwalejen ‘yan gata ta ENA. A nan ne ta sadu da Francois Hollande shugaban jam’iyyar Socialist wanda suke da ‘ya’ya hudu tare da shi. A cikin shekarun 1980 ta zama wata jami’a mai ba da shawara ga tsofon shugaban kasar Faransar marigayi Francois Mitterrand kafin ta wayi gari a matsayin ministar muhalli, ilimi da zamantakewar iyali. Ta taimaka wajen bai wa maza damar daukar hutu na renon yara. Kazalika ta taka rawar gani a matsayin mace mai kula da renon ‘ya’yanta ba tare da tayi sako-sako da sana’arta ba. Ta samu gagarumar nasara ne a shekarar 2004 lokacin da ta samu galaba a yankin Poitou-Charentes dake yankin kudu maso yammacin Faransa. A nan ne ta fara gwada manufarta, wadda take fatan aiwatarwa a duk fadin kasar Faransa. Segolene Royal ta ce:

“Kakkarfan matsayin da nike da shi shi ne na kawo canji a cikin ruwan sanyi, ina kuma kaunar wani tsari mai adalci.”

A yayinda magoya-bayanta ke yaba mata da zama mace mai sara tana duban bakin gatari, abokan adawarta na zarginta da neman suna. A dai halin da ake ciki yanzun Segolene Royal na tattare da imanin cewar kasancewarta mace, abu ne da zai ba ta wata cikakkiyar dama ta zama shugabar kasa, tana mai yin kira ga illahirin matan kasar Faransa da su ba ta goyan baya.