Segolène Royal yar takara jama´iyar PS a zaɓen shugaban ƙasar France | Labarai | DW | 17.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Segolène Royal yar takara jama´iyar PS a zaɓen shugaban ƙasar France

Yan jama´iyar gurguzu wato PS, na ƙasar France, sun tsaida Segoléne Royal, a matsayin yar takara, a zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana,shekara mai zuwa.

Bayan sati 7, na yaƙin neman zaɓe, da mahaurori tsakanin yan takara 3 , sai ranar jiya, wakilan jam´iyar a sassa daban-daban na ƙasa su ka raba gardama.

Sakamakon ƙuri´un ya ba Segolene Royal, fiye da kashi 60 bisa 100, sai tsofan ministan tattalin arziki Dominique Strauss-Khan, da ya samu kussan kashi 20 bisa 100, sannan daga ƙarshe tsofan Praminista Lauran Fabius, ya tashi da kimamnin kashi 18 bisa 100, na yawan ƙuri´un da aka jefa.

Jim kaɗan bayan bayana wannan sakamako, yan takara 2 da su ka sha kayi, su ka yi kira ga magoya bayan su, su bada haɗin kai, ga Segolene Royal, domin jam´iyar PS ta cimma burin lashe zaɓen shugaban ƙasar.

Jaridu a France, sun nunar da cewa, wannan zaɓe na matsayin babban ƙalu-bale ,ga ɗan takara jama´iyar UMP mai riƙe da ragamar mulki, wato Nicolas sarkozy ministan cikin gida.