1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Schulz yana da masaniya kan Afirka

January 31, 2017

A Jamus Jam'iyyar SPD ta tsayar da Martin Schulz tsohon shugaban majalisar Turai domin fafatawa da Angela Merkel a zaben watan Satumba mai zuwa, ana sharhi makomar dangantakar Jamus da Afirka idan Schulz ya yi nasara.

https://p.dw.com/p/2Whst
Berlin SPD PK Martin Schulz Kanzlerkandidatur
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Dan takarar da jam'iyyar ta SPD ta tsayar da zai fafata da Merkel a zaben 'yan majalisar ta tafe dai mutun ne da ya san Afirka bakin gwargwado kasancewa ya ziyarci nahiyar ba sau daya ba a lokacin da yake jagorancin Majalisar Turai. A shekarar ta 2013 sai da ta kai shi ga ziyartar taron majalisar dokokin Afirka da ke da cibiyarta a Afirka ta Kudu inda har ma ya gabatar da jawabi a gaban 'yan majalisar ta Afirka, jawabin da ya jaddada aniyar Tarayyara Turai ta EU na tallafa wa majalisar dokokin ta Afirka da aka kafa a shekara ta 2004.

Berlin SPD PK Martin Schulz Kanzlerkandidatur
Hoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Kazalika a shekara ta 2016 ya kai ziyara a kasar Tunusiya inda ya jinjina wa kasar yadda tsarin mulkinta mai jam'iyyun barkatai ke tafiya cikin fahimta da hakuri da juna tsakanin 'yan siyasar kasar.Nan ma ya sha alwashin tallafa wa kasar wajen tabbatar da doka da oda dama kyautatuwar 'yancin fadin albarkacin baki.Ana Gomes 'yan majalisar dokokin kasar Portugal mamba  akwancan jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayin gurguzu na Socio-Democrates a majalisar Turai ta yi karin haske kan dangantakar Martin Schulz da nahiyar ta Afirka, inda yake ganin Schulz a matsayin mai neman ganin sauyi na bunkasa a nahiyar ta Afirka.

Deutschland Martin Schulz Europawahlkampf der SPD in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Burgi

A halin yanzu dai bayan da ya bar mukamin shugabancin majalisar Turan, Martin Schulz na fatan ganin ya maye gurbin Angela Merkel daga kan kujerara shugabancin  gwamnatin kasar ta Jamus wacce za ta neman yin tazarce kanta a karo na biyar. To sai dai ayar tambaya ita ce wace riba Afirka za ta samu daga jagorancinsa idan har ya yi nasarar kayar da Angela Merkel wacce gwamnatinta ta kaddamar da wani sabon shiri na tallafa wa kasashen Afirka da ake yiwa lakabin Afrika Marshall Plan. Grit Lenz shugabar kungiyar Fokus Sahel mai aikin bincike kan siyasar kasashen Sahel na ganin ko ma Schulz ya yi nasarar maye gurbin Angela Merkel da wuya ya y yin watsi da wannan shiri na Afrika Marshall Plan.

Yanzu 'yan kasar ta Jamus dama kasashen Afirka sun zura ido kan wanda zai lashe zaben na watan Satumba tsakanin Angela Merkel da Martin Schuls. Sai dai kafin zuwa wannan zabe ne Jamus za ta shirya wani taron koli kan batun bunkasa nahiyar Afirka.