1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Schröder A Saudiyya

February 28, 2005

A matakin farko a ziyararsa ga kasashen Larabawa, shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya gana da shuagabannin kasar Saudiyya

https://p.dw.com/p/Bvcy
Schröder a Saudiyya
Schröder a SaudiyyaHoto: dpa

Tun a jiya lahadi shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya gana da Yerima Abdallah da Sarki Fahad, sannan a yau litinin da sanyin safiya ya gabatar da jawabi ga wani taron 'yan kasuwa na Jamus da na Larabawa. Rahotanni sun nuna cewar a lokacin ganawar tasu da sarki Fahad dake fama da rashin koshin lafiya, shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya ba wa shuagabannin saudiyyar kwarin guiwar ci gaba akan manufofinsu na garambawul. Schröder ya ce ko da yake ana fama da tafiyar hawainiya, amma akalla ana sammun ci gaba sannu a hankali akan manufa. Dangane da manufofin ketare kuwa shuagabannin sun tattauna ne akan rikicin Iraki da na Isra’ila da Palasdinawa. Dukkan sassan biyu, kamar yadda majiyoyi masu nasaba da tawagar wakilan gwamnatin Jamus suka nunar, sun hakikance da muhimmancin rawar da Amurka zata iya takawa a fafutukar neman zaman lafiyar Yankin Gabas ta Tsakiya. Amma duk da haka Yerima Abdallah mai jiran gado yayi godo ga Jamus da ta kara yawan gudummawar da take bayarwa wajen sake gina yankunan Palasdinawa dake da ikon cin gashin kansu. Sai dai kuma bisa sabanin yadda aka tsammata da farko, a lokacin ganawar ba a tabo shirin tashoshin nukiliyar Iran ba. Da farko an yi batu a game da cewar shugaban gwamnati Gerhard schröder zai nemi goyan baya daga kasashen yankin Gulf a shawarwarin da ake yi da kasar Iran. Muhimmin abin da shugaban gwamnatin na Jamus ya fi ba da la’akari da shi shi ne dangantakar tattalin arzikin kasar da kasar saudiyya, kuma ga alamu ganawar da suka yi da yerima Abdallah ta kara ba shi kwarin guiwa akan wannan manufa. Domin kuwa bayan ganawar an saurara daga Schröder yana mai bayanin cewar kasar Saudiyya, kasa ce dake da dimbim arzki da yalwa da kuma wata kyakkyawar dama ta zuba jarin kamfanonin Jamus a cikinta. A baya ga hadaddiyar daular Larabawa, kasar saudiyya ce babbar abokiyar burmin cinikin Jamus a tsakanin kasashen Larabawa, ko da yake an fara samun koma baya a wannan dangantaka. Yawan kayayyakin da Jamus ke fitarwa zuwa Saudiyya ya ragu da misalin kashi takwas cikin dari tun daga shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2004. Amma duk da haka ‚yan kasuwar Jamus na fatan samun kwangila mai tsoka, musamman wajen gina hanyoyin sadarwa a kasar ta Saudiyya. A lokacin shagulgulan bude bikin baje kolin shekaru 75 da kulla yarjejeniyar kawancen Jamus da Saudiyya, shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi godo ga matasa na Saudiyya da su rika neman karin ilimi a Jamus. Ya ce gwamnati zata tanadar da wani shirin skolaship akan wannan manufa. Kazalika ya kuma yi kiran karfafa dangantakar al’adu tsakanin sassan biyu. Ya ce kawance ba ta tabbata sai a tsakanin mutanen dake fahimta da kuma girmama juna da kuma ma’amalla tsakani da Allah.