Schröder A Qatar | Siyasa | DW | 02.03.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Schröder A Qatar

A ziyararsa ga kasar Qatar shugaban gwamnatin Jamus Gerhard schröder yayi nuni da kakkarfar dangantakar siyasar dake akwai tsakanin kasashen biyu

A lokacin da suka gana da sarki Scheich Hamid bin Khalifa Al-Thani na kasar Qatar, shugaban gwamnatin Jamus yxa hakikance da gaskiya cewar Jamus dai ta zo a makare, amma duk da haka lokaci bai kure ba domin neman kwangila ga kamfanoninta. An dai saurara daga bakin Schröder yana mai bayanin cewar:

Muhimmin abin da muka mayar da hankali kansa a tattaunawarmu shi ne batutuwan tattalin arziki, saboda ba mu da wata matsala a dangantakarmu ta siyasa. Bisa sabanin haka, dangantaka tsakanin Jamus da Qatar na tafiya salin alin ba tare da wata tangarda ba.

A fanin tattalin arziki kuwa, kamfanin Jamus mai suna Uhde ya samu kwangilar Euro miliyan 500 domin gina wata masana’antar dake sarrafa tabn dubu 2 na takin zamani a kowacve rana ta Allah a kasar ta Qatar, lamarin dake yin nuni da kakkarfan hadin kan dake akwai tsakanin kasashen biyu. Daidai da ziyararsa ga kasashen Saudiyya da Kuwait, a can Qatar ma shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi kiran fadada huldar tattalin arzikin domin ta hada da bangaren makamashi da hidimomin kyautata jin-dadin rayuwar jama’a. Wasu daga cikin ‚yan kasuwar dake wa shugaban gwamnatin na Jamus rakiya sun saka fatan cewar za a cimma daidaituwa a game da gina hanyar dogo mai nisan kilomita 800 daga Qatar zuwa hadaddiyar daular Larabawa, domin amfanin jirgin kare gudunka na Transrapid kirar Jamus. Schröder ya ce kamfanonin jamus suna da gagarumar kwarewa wajen gina irin wannan hanyar dogo da kuma fasahar aiwatar da jirgin mai maganadisu. Kasar a shirye take ta taimaka wajen tsarawa da kuma wanzar da wannan shiri saboda nagartacciyar fasahar da Allah Ya fuwace mata. Schröder ya yaba da irin ci gaban da kasar ta qatar ta samu da kuma yadda take ba da fifiko wajen ilimantar da mata domin kama sana’o’in hannu ta yadda zasu iya dogara da kansu. A dukkan shawarwarin da Schröder ya gudanar da shuagabannin kasashen na Larabawa da yake kai wa ziyara sai an tabo maganar yankin gabas ta tsakiya da rikicin Iran da kuma takaddamar da ake famar yi da kasar Iran. Ga alamu wadannan batutuwan ne zasu ci gaba da mamayar shawarwarin da zai gudanar da shuagabannin kasar Bahrein kafin ya zarce zuwa kasar Yemen a yammacin yau laraba.