Sauyin yanayi ka iya gurgunta tattalin arzikin duniya | Labarai | DW | 31.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sauyin yanayi ka iya gurgunta tattalin arzikin duniya

Wani rahoto da gwamnatin Birtaniya ta bayar yayi gargadin cewa dumamar doron kasa ka iya janyo kaura ta miliyoyin mutane tare da gurgunta tattalin arzikin duniya baki daya. FM Birtaniya Tony Blair ya gabatar da sakamakon binciken da tsohon masanin tattalin arziki na bankin duniya Nicholas Stern yayi inda a ciki ya nunar da cewa dumamar yanayi ka iya janyowa duniya asarar kudaden da ya kai kashi 20 cikin 100. Babbar sakatariyar MDD mai kula da sauyin yanayi dake nan birnin Bonn, ta nunar da cewa iska mai guba da kasashe masu ci-gaban masana´antu ke fitarwa ta karu da kashi 2.4 cikin 100 daga shekara ta 2000 zuwa ta 2004. Hakan ta samu ne saboda shirye shiryen ta da komadar tattalin arziki da ake dauka a tsofaffin kasashen kwaminis na gabashin Turai. Yarjejeniyar birnin Kyoto ta tanadi rage iskar mai guba da kashi 5 cikin 100 idan aka kwatanta da yawan ta a shekarar 1990.