1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauye sauye ga zaman tarayya a jamhuriyar Jamus

June 30, 2006
https://p.dw.com/p/BusD

Tare da rinjayen kashi 2 cikin 3, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta kada kuri´ar yiwa tsarin zaman tarayyar kasar kwaskwarima. Ana kwatanta wannan canje canjen da cewa shi ne mafi muhimmanci tun bayan kirkiro tarayyar ta Jamus a cikin shekarar 1949. Canje canjen da aka dade ana sa ran aiwatarwa an tsara shi ne da nufin sake fasalta dangantaka tsakanin gwamnatin tarayyar da gwamnatocin jihohin kasar ta Jamus. Su dai jihohin kasar sun amince zasu janye wani bangare na ikon da suke da shi a majalisar shawara ta tarayya sannan a saka musu ta hanyar ba su cikakken ikon tafiyar da makarantu da kuma ´yancin ma´aikatan hukuma. A cikin mako mai zuwa majalisar shawarar zata kada kuri´a akan sabon tsarin na zaman tarayya.