Sauraron ci gaba da shari´ar da akewa Saddam Hussain | Siyasa | DW | 28.11.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sauraron ci gaba da shari´ar da akewa Saddam Hussain

An kara dage sauraron shari´ar izuwa biy

Wani mutumin iraq

Wani mutumin iraq

Jim kadan da zaman wannan kotu,rahotanni sun shaidar da cewa kotu tayi dan shiru na dan mintoci kadan don tunawa da kuma nuna alhini ga wasu lauyoyi dake kare wadanda ake tuhuma a sakamakon rasa ransu da suka yi.

Bayan haka ne kuma sai kotun ta bayar da umarnin saka kaset din bidiyo na farko dake dauke da hoton bidiyo na mai bada shaida, wanda yake tsohon ma´aikacin leken asiri ne na kasar, wanda kuma tuni Allah yayi masa rasuwa a sakamakon ciwon kansar daya same shi.

Idan dai za a iya tunawa a zaman wannan kotu na farko a sha tara ga watan oktoba, tsohon shugaban kasar ta Iraqi wato Saddam Hussain da ragowar mutane bakwan dukkannin su sun karyata cajin da ake musu.

Abubuwan da ake tuhumar su da aikatawa dai sun hadar da kisan kiyashi da dandanawa mutane azaba da kuma take hakkokin su a lokacin zamanin mulkin tsohon shugaban.

A takaice dai ana zargin tsohon Shugaba Saddam Hussain da kisan mutane yan darikar shi´a kusan 140 a garin Dujail a shekara ta 1982, lokacin da aka zarge su da yunkurin kisan tsohon shugaban na Iraqi.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa Saddam Hussain ya iso cikin wannan kotu ne sanye da kwat da kuma farar shirt a jikinsa.

A dai lokacin wannan zama a birnin na Bagadaza daya samu tsauraran matakan tsaro, bayanai sun shaidar da cewa anyi musayar miyau mai tsananin gaske a tsakanin alkalin kotun da kuma Saddam Hussain.

A lokacin wannan musayar miyau, Saddam ya gabatar da korafi ne ga alkalin kotun game da yadda yake fuskantar wulakanci, a inda ya kawo misali da cewa koda a yau din nan sai da aka biyo dashi ta kafar bene mai hawa hudu tare da jamian tsaro na binsa a baya.

Jim kadan da gabatar da wannan korafi nasa, sai Alkalin kotun yace zai shaidawa jamian yan sanda dasu daina wulakanta shugaban.Jim kadan da fadin haka sai Saddam Hussain ya nuna hannu da cewa sai ka shaida musu.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa lauyoyin dake kare Saddam Hussain a wannan shari´a sun bukaci da a dage zaman wannan kotu izuwa watanni uku a sabili da rashin tsaro da ba a dashi a birnin na Bagadaza da kuma ma kasar ta Iraqi.

To amma a maimakon Alkalin kotun, wato Mohd Amin ya dage sauraron karar izuwa hakan, sai ya dage ta izuwa biyar ga watan disamba na wannan shekara da muke ciki, don bawa daya daga cikin wadanda ake tuhuma, wato Taha yassin Ramadan dama na samun lauyan da zai kare shi.

A can baya dai Taha Yassin Ramadan yayi watsi da lauyan da kotun tace zata bashi a sakamakon rasuwa da lauyan da yake kareshi yayi

Ya zuwa yanzu dai masu nazarin siyasa na gani8n cewa da alama wannan sharia ka iya kaiwa izuwa shekaru masu yawa ana gudanar da ita, a sabili da irin tafiyar hawainiya da akeyi a hannu daya kuma da sabbin caji da aka fito dasu a kann wadanda ake tuhumar.

 • Kwanan wata 28.11.2005
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu3u
 • Kwanan wata 28.11.2005
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu3u