1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Raul: Zan ci gaba da akidar Fidel Castro

December 4, 2016

Dubban jama'a sun yi dafifi a Santiago domin ban kwana da kuma karrama tsohon shugaban Cuba Fidel Castro yayin da za a binne tokar gawarsa a wannan lahadin a birnin na Santiago.

https://p.dw.com/p/2Thlt

Shugaban kasar Cuba Raul Castro ya sha alwashin ci gaba da akidar gwagwarmayar juyin juya hali na dan uwansa Fidel Castro a wani gagarumin gangami da aka yi na karrama marigayin kafin a binne tokar gawarsa. Dubban jama'a sun hallara dauke da tutoci su na rera wakokin gwagwarmyar juyin juya hali da ke tunato da gudunmawar da marigayi Fidelo Castro ya bayar wajen cigaban kasar.