A cikin shirin za a ji kasar Chadi ta janye sojojinta daga Niger inda suke taimakawa wajen yaki da 'yan Boko Haram. Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Najeriya ta biya diyya ga wasu mata hudu da jami'an tsaro suka bata wa suna da kuma tsare su kan zargin karuwanci.