Saura kai | Learning by Ear | DW | 31.07.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Saura kai

default

Saura kai.


Shirin Ji ka karu yana so ya ji daga gare ka kai tsaye, inda muka yi kuskure a gaya mana in akwai abin da muka manta a tunasar da mu, inda muka cancanci yabo, a yaba mana. Ku rubuto mana a game da yadda kuka fuskanci al'amura a rayuwarku ta yau da kulum kan fannonin da muka gabatar da shirye-shiryemmu a kansu.

Sai mun ji daga gare ku.

Laminu Musa, Maraɗi, Jamhuriyar Nijer (mousslami@yahoo.com)

Na yi matuƙar farin ciki da shirinku na Ji ka Ƙaru akan mayar da duniya tsinsiya maɗaurinki ɗaya, musamman ma dai yadda kuka bayyana mana tsarin noman yarjejeniya, da kuma yadda ake ƙulla alaƙa tsakanin manoma da kuma manyan kamfanoni da suke cinikayyar amfanin gona da abinci.

Malam Ango Yawuri, Najeriya (mallanango@yahoo.com)

DW Allah ya saka muku da alheri, na yi farin ciki da shirin Ji Ka Ƙaru wanda akai batu game da tsarin mayar da duniya bai ɗaya. To amma tamabayata ita ce; Shin idan aka mayar da duniya bai ɗaya, kuɗi ɗaya duka ƙasashen duniya za su riƙa amfani da su ko kuwa yaya abin yake.

Kabir Sakaina layin ‘yan goro Malumfashi, Katsina Najeriya.

(kabeersakaina@gmail.com)

Shirinku na Ji Ka Ƙaru akan tsarin noma na adalci ba cuta ba cutarwa, shiri ne da yake da matuƙar ƙayatarwa da ilimanatarwa. Da fatan sashen Hausa na DW zai tsara dukkanin shirye-shiryenku na Ji Ka Ƙaru a faya-fayai da kaset-kaset ku aika ga gidajen rediyo da dama na jaridu da mujallu a nahiyar Afirka. Domin a gaskiya waɗannan shirye-shirye amfaninsu ba mai ƙarewa ba ne, don haka bai kamata a ce wadannan shirye-shirye masu ma'ana daga an watsa su sau ɗaya shi ke nan sun tafi ba.

Salamatu Yusuf Dodo Najeriya (salma12@yahooo.com)

DW Ina mai tabbatar muku da cewa, shirinku na Ji Ka Ƙaru ya sa kun zarce sa'a, mu dai a wajenmu ba ku da na biyu. Gaba dai gaba dai radiyo DW.

LINK: http://www.dw-world.de/dw/article/0,,3527925,00.html

 • Kwanan wata 31.07.2008
 • Mawallafi Mohammed, Zainab
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/DrI4
 • Kwanan wata 31.07.2008
 • Mawallafi Mohammed, Zainab
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/DrI4