1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya da Rasha na fatan karfafa dangantaka

Abdullahi Tanko Bala
October 5, 2017

Shugaban Rasha Vladimir Putin da Sarki Salman na Saudiyya na fatan hada hannu domin samar da daidaito kan farashin mai a duniya da kuma inganta al'amuran tsaro

https://p.dw.com/p/2lH1O
Türkei Putin und König Salman bin Abdulaziz Al Saud
Hoto: picture alliance/dpa/M. Klimentyev

Ziyarar wadda ke zama ta farko da sarki Salman ya kai Rasha na da nufin kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Putin da sarki Salman sun tattauna kan batutuwan da suka hada da kasuwar mai a duniya da kuma yakin Siriya.

Sau da dama dai dangantaka tsakanin kasashen biyu ta na tsami a baya.

A lokacin yakin cacar baka Saudiyya ta taimaka wajen baiwa 'yan tawayen Afghanistan makamai a yaki da tarayyar Soviet.

A baya bayan nan kuma tsamin dangatakar ta yi kamari kan yakin Siriya inda Rasha ta mara baya ga shugaba Bashar al Assad yayin da Saudiyya kuma ta goyi bayan masu adawa da shi.

Ana sa ran bangarorin biyu za baiyana kulla harkar kasuwanci ta miliyoyin daloli.