1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudi ta nada sabon ministan mai

Sanarwa daga masarautar kasar mai albarkatun man petur, na nuni da cewar an maye gurbin Ali al-Naima da ministan kula da lafiyan kasar Khaled al-Falih.

A ci-gaba da tankade da rairaya da hukumomin Saudi ke yi, a wannan Asabar ceaka sanar da sauke ministan mai da ya kwashe shekaru 20 ya na kan wannan mukami.

Kafin sauke shi a yau din dai, al-Naima ya kasance mutumin da ke da wuka da nama a kan dukkan batutuwa da suka shafi mai, tare da jagorantar ma'aikatar albarkatun man kasar tun daga shekara ta 1995.

A karkashin sabuwar gwamnatin kasar ta Sarki Salman, an yi imanin cewar mataimakin danshi kuma kuma yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, shi ne ke kula da akalar harkokin da suka shafi ma'aikatu, da ma mafi yawa daga cikin sabbin ministocin.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar take shirin yin wasu sauye-sauye game da tattalin arzikin kasar da a baya ya ta'allaka a kan albarkatun man petur da yanzu kasuwarsa ta fadi.