1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin manoma da makiyaya a Najeriya

Abdullahi Maidawa Kurgwi / LMJJune 3, 2016

A wani mataki na ganin an kawo karshen yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya, gwamnatin jihar Filato ta ce ta dauki matakan fidda labin shanu a sassan jihar daban- daban.

https://p.dw.com/p/1J0HM
Hoto: GTZ / Dirk Betke

Wannan dai shi ne karon farko da wata gwamnati a jihar Filato ta amince da batun kafa labin shanu kasancewar an shafe shekaru da dama ana kai ruwa rana tsakanin manoma da makiyaya, lamarin da ya janyo asarar dimbin rayuka da dukiyoyin jama'a a shekarun baya. Mohammad Nazifi, shi ne kwamishinan watsa labarai na jihar Filato, ya ce tuni ma har wasu al'ummomin yankunan kananan hukumomin jihar ta Filato suka amince za su bada filayensu domin bude labin.

Somalia Äthiopien Viehzucht-Nomaden
Hoto: DW/J. Jeffrey

Wannan sabon shirin dai jama'ar jihar da dama basu fahimce shi ba. To ko ya suke kallon wannan mataki, Injiya Daniel kazai wani shugaban al'umma ne ya ce muddin gwamnati ba za ta kwace filiye na jama'a da sunan kirkiro da labin shanun ba, wannan tsari ne mai amfani.

Makiyaya sun yi maraba da batun

A bangare guda kuma makiyayan jihar sun ce suma sun gaji da yawace- yawace da sunan kiwo, don haka sun yi maraba da wannan mataki muddin gwamnatin jihar ba wai za ta yi musu shigo-shigo ba zurfi ba ne kan lamarin. Yanzu dai an soma samun saukin tashin hankali a tsakani manoma da makiyaya a jihar Filato abin jira a gani shi ne yadda wannan sabon tsari na gwamnati zai taimaka wajen dorewar zaman lafiya tsakanin manoman da fulani makiyaya.