1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy zai buɗe taron Faransa da Afirka

May 28, 2010

A makon gobe za'a gudanar da taron shugabannin Afirka a ƙasar Faransa domin tattauna hulɗar kasuwanci

https://p.dw.com/p/NcLK
Shugaban Faransa Nicolas SarkozyHoto: AP

A mako maizuwa ne Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy zai gana da wasu shugabannin Afirka da nufin tattauna haɗin kai da cigaban juna a garin Nice dake Faransa.

Taron na kwanaki biyu zai samu halartan shugabannin ƙasashen Najeriya da Afirka ta kudu da Rwanda da Nijer da kuma Habasha. Shekaru uku da hawansa kan mulki ne dai shugaba Sarkozy ya fara shirya wannan gagarumin taro tsakanin Faransa da kuma wasu ƙasashe na Afirka da nufin ƙara danƙon zumunci da ɓunƙasar tattalin arzikin juna.

Kanfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar bayan wayannan shugabanin na Afirka su 40 da zasu halarci taron, akwai kuma 'yan kasuwan Faransan su kimanin 80 da zasu hallara tare da takwarorinsu na Afirkan 150.

Tun bayan saukan tsohon shugaban Faransa Jacques Chirac daga mulki ne dai dangantaka tsakanin Faransa da nahiyar Afirka yaja baya matuƙa.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Muhammad Nasir Awal