Sarkozy ya yi kira ga sake fasalin MƊD. | Labarai | DW | 11.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarkozy ya yi kira ga sake fasalin MƊD.

Shugaban Faransa ya buƙaci fa'ɗaɗa kwamitin sulhun MƊD.

default

Shugaba Sarkozy na gabatar da jawabi.

Shugaba Nikolas Sarkozy na ƙasar Faransa, ya yi kira ga sake fasalin Majalisar Ɗinkin Duniya, kana ya buƙaci tattaunawar da gungun wasu ƙasashe ƙalilan ke yi ta hanzarta ƙoƙarin yaƙi da sauyin yanayi a duniya. A lokacin da yake buɗe wani babban taron yini ɗaya akan sare dazuzzuka, Sarkozy yace, ko da shike Majalisar Ɗinkin Duniya na taka rawar gani ta fuskar zama wanin zauren da ƙasashen duniya baki ɗaya ke hallara, su tofa albarkacin bakinsu game da abubuwan da suka shafi duniya kuma a sauraresu - ko da sun ci gaba ne ko kuma matalauta, amma ya ce, yana da yaƙinin cewar abubuwa basa tafiya yanda ya dace, kuma a cewarsa - idan ba'a samar da sauye sauyen ba, to, kuwa za'a wayi gari Majalisar ta kasance wurin da ba za'a taɓa cimma matsaya ba. Akan hakane shugaban na Faransa ya jaddada shawarar faɗaɗa kwamitin sulhun Majalisar, da ƙara yawan mambobinsa, kana da keɓe kujeru ga nahiyoyin duniya daba daban. Shugaban ya yi Allah wadai da sakamakon babban taron duniya kan sauyin yanayin da aka yi cikin watan Disambar bara - a birnin Copenhagen na ƙasar Denmark, yana mai ɗora alhakin gazawar taron akan rashin kyakkyawan jagoranci.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Muhammad Nasir Awal