Sarkozy, mai takarar neman zama shugaban kasa a faransa | Siyasa | DW | 18.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sarkozy, mai takarar neman zama shugaban kasa a faransa

Sarkozy dan takara ne dake neman mayewa gurbin shugaba Jacquse Chirac

Nicolaus Sarkozy

Nicolaus Sarkozy

Nicolaus Sarkozy dai mai azama kuma yayi fice a harkokin siyasa. Abokan adawarsa kan zarge shi da kwadayin mulki da babakere. Sarkozy dai bai yi sako-sako ba wajen kara inganta martabarsa a idanun jama’a a matsayinsa na dan takarar neman zama shugaban kasa a Faransa. An saurara daga bakinsa yana mai bayanin cewar:

“A ganina duk wani mtum mai karfin zuciya bai kamata ya nuna wata halayya ta gazawa ba. Na lura cewar bai karfi zuciya shi ne mai magana tsakani da Allah ba tare da wata rufa-rufa ba. Bugu da kari nuna halin sanin ya kamata da kuma tausayawa ba gazawa ba ne.”

Sarkozy dai fitacce ne a sana’arsa ta siyasa. Ana iya lura da haka a salon maganganunsa da dai sauran take-takensa a duk lokacin da ya fito bainar jama’a. A takaice Sarkozy mutum ne mai hazaka wanda kuma likafarsa tayi gaba a cikin gaggawa bayan kama sana’ar siyasa. Ga dai abin da yake cewa:

“Tun ina dan shekara 15 zuwa 16 da haifuwa na fara sha’awar shiga siyasa. A hakika ma dai ba ni ne na zabi siyasa ba, siyasa ce ta zabe ni. Ina sha’awar rayuwa mai kazar-kazar ta kuma cimma wata manufa a rayuwata.”

Sarkozy, wanda mahaifinsa dan kaka-gida ne daga kasar Hungary, ya nazarci ilimin shari’a kafin ya shiga tutar jam’iyyar RPR mai ra’ayin sake raya manufofin janar de Gaul. Tsofon shugaban jam’iyyar Jacques Chirac ya bai wa matashi Sarkozy cikakken goyan baya a wancan lokaci. Yana dan shekaru 28 da haifuwa aka nada shi magajin garin Neuilly-sur-Sein dake kusa da birnin Paris inda ya sadu da matarsa Cecilia. A halin yanzu haka suna da ‘ya’yan maza guda uku, wadanda ya ce duka-duka gargadin da yake musu shi ne su dauki aiki da muhimmanci. Shi kansa ba ya sako-sako da motsa jiki kuma ba ya shan giya. Sarkozy, wanda duka-duka tsayinsa mai wuce tsawon mita daya da digo 65 ba, ya rike mukamai daban-daban da suka hada da ministan tattalin arziki, kudi da masana’antu, kuma sau biyu yana rike mukamin ministan cikin gida na kasar Faransa. Yana ba da cikakken goyan baya ga kare doka da oda. Kuma bai taba rufa-rufa a game da kwadayinsa na zama shugaban kasar Faransa a fadar mulki ta Elysee ba.