sarki Mohamed na Marroko ya aika saƙwan barka da Maulidi ga ƙasashen musulmi. | Labarai | DW | 01.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

sarki Mohamed na Marroko ya aika saƙwan barka da Maulidi ga ƙasashen musulmi.

Albarakacin bikin Maulidin Manzan Allah, tsira da amincin Allah, su ƙara tabbata a gare shi, Sarki Mohamed na Marroko, ya aika wasiƙu ga shugabanin ƙasashen musulunci na dunia.

Mai Martaba Sarki ya bayana fallala da rahamar da su ka samu a dunia albarkacin aihuwar Manzan Allah.

Sannan yay kira ga musulmin dunia su zama tsintsiya maɗaurin ɗaya, domin fuskantar ƙalubale da musulunci ke fuskanta, daga wassu sassa na dunia.

Sarki Mohamed, yayi Allah wadai ga masu danganta addinin musulunci da ta´adanci, da abubuwa masu kama da haka.

Sannan wasiƙar ta gayyaci musulmi, su himmantu, wajen zama na cuɗe ni in cuɗe ka, tare da sauran addinai, na dunia.