Sarki Abdullah zai gana da Mahmud Abbas da Isma´il Haniya | Labarai | DW | 26.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarki Abdullah zai gana da Mahmud Abbas da Isma´il Haniya

Majalisar ministocin FM Isra´ila Ehud Olmert ta amince a kawad da wuraren da aka toshe hanyoyi har 27 dake Gabar Yamma da Kogin da ke karakshin mamayen Isra´ila. Wannan mataki na daya daga cikin alkawuran da FM Olmert ya yiwa shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. Hakan zai ba da damar yin jigilar kayayyaki cikin yankunan na Yammacin Kogin Jordan inda aka toshe hanyoyi da kakkafa daruruwan wuraren binciken ababan hawa. A halin da ake ciki Abbas ya na birnin Amman inda zai gana da sarki Abdullah na Jordan, wanda ya fara wani yunkurin yin sulhu tsakanin Abbas da FM Falasdinawa Isma´il Haniya. Rahotanni sun nunar da cewa Haniya zai je birnin na Amman don amsa gayyatar sarki Abdullah.