Sarauniyar Ingila ta buƙaci haɗin kai | Labarai | DW | 07.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarauniyar Ingila ta buƙaci haɗin kai

Sarauniyar Ingila Elizabeth, ta buƙaci kawar da hatsarin da duniya ke fiskanta

default

Sarauniya Elizabeth ta biyu a zauren MDD

Akaro na farko Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu, tun shehkaru fiye da 50, ta yi jawabi a gaban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya. Sarauniya Elizabeth ta buƙaci majalisar da ta ci gaba da taka mahimmiyar rawa a hatsarin da duniya ke fiskanta, da kuma kawo ci gaba. Sarauniyar Ingila dake da shekaru 84 a duniya, ta bayyana yadda ta ga Majalsar ta Ɗinkin Duniya ta samu sauyi, bayan da ta yi waiwaye a shekarun baya da ta yi magana a zauren majalisar, lokacin da take buduruwa. Inda ta yi ƙira da a ci gaba da haɗa hannu a nan gaba don samar da cigaban tattalin arzikin duniya. Ta kuma aza furen girmamawa a filin da aka kai harin ta'addanci a ranar sha ɗaya ga watan satumba.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu