Santos zai zama shugaban ƙasar Colombia
June 21, 2010Tsohon ministan kula da harkokin tsaron ƙasar Columbia, Juan Manuel Santos ya sami rinjaye a sakamakon zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Columbiar daya gudana a jiya Lahadi, domin ya gaji shugaban ƙasar Alvaro Uribe. A yayin da aka kammala ƙidaya kashi 98 cikin100 na ƙuri'un da al'ummar ƙasar suka ka'ɗa a tashoshin zaɓe, Santos ya yi nasarar samun kashi 69 cikin100, inda ɗan takarar dake rufa masa baya a yawan ƙuri'u kuma, wato tsohon magajin garin Bagota, kana ɗan takar jam'iyyar Greens, Antanas Mockus ya sami kimanin kashi 27 da rabi cikin 100 na ƙuri'un. Santos, wanda shugaba Uribe - mai barin gado ke mara masa baya, ya ci alwashin bi sau - da - ƙafa manufofin da shugaban ke aiwatarwa a sha'anin tsaro da kuma samar da kyakkyawan yanayi ga harkokin kasuwanci, manufofin da kuma suka janyo ɗimbin masu zuba jari daga ƙetare zuwa ƙasar.
Mawallafi :Saleh Umar Saleh
Edita : Abdullahi Tanko Bala