Sankarau na ci gaba da kisa a Najeriya da Nijar
May 12, 2017A cewar rahoton kungiyar ta Medicine Sans Frontairs a turancin faransa, akalla mutane 10,000 ne suka kamu da cutar ta sankarau rukunin C wadda kuma ita ce mafi hatsari a Najeriya a wannan shekara kadai.
Rahoton ya ce jihohin Sokoto da Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya ne cutar ta fi kamari cikinsu a kwanakin baya, inda masu kamuwa da ita kan rasa karfin garkuwar jiki, da raunin kwakwalwa da kuma na laka.
Hukumomi a tarayyar ta Najeriya dai na bayyana nasarar kakkabe cutar baki daya, amma ga alama akwai sauran rina a kaba. A wata ziyara da DW ta kai kauyen Bagarawa na karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto, mutanen kauyen sun ce har yanzu cutar na nan cikin jama'a.
Rahoton na Medicine Sans Fronteirs, haka nan ya bayyana shakku a kan karancin magungunan sabuwar cutar da aka yiwa lakabi da type C a dai dai lokacin da cutar ke ci gaba da kashe mutane. Ko a kwanakin nan ma inji mazauna kauyen Bagarawa an rasa rayuka a sakamakon wannan cuta.
Sai dai a ta bakin kwamishinan lafiya na jihar Sokoto Dr. Balarabe Shehu Kakale, sankarau ta zama tarihi a jihar Sokoto idan aka yi la'akari da kwararan matakan da gwamnati ta dauka.
Cutar ta sankarau dai cuta ce mai saurin yaduwa da kisan jama'a cikin hanzari.