Sanarwar Gwamnati Akan Daftarin Tsarin Mulkin Kasashen Turai | Siyasa | DW | 02.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sanarwar Gwamnati Akan Daftarin Tsarin Mulkin Kasashen Turai

A zaman mahawarar da suka gudanar a yau juma'a dukkan wakilan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag sun yi marhabin da daftarin tsarin mulki bai daya na kasashen Turai

Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder

Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder

Dukkan wakilan gwamnati da na ‚yan hamayya suka yaba wa daftarin tsarin mulkin bai daya tsakanin kasashen Turai, wanda suka ce wata manufa ce ta tarihi. A lokacin da yake ba da sanarwar gwamnatinsa Gerhard Schröder cewa yayi:

Bisa ga ra’ayi na wannan kuduri da aka cimma dangane da daftarin tsarin mulki wani muhimmin ci gaba ne a fafutukar tabbatar da hadin kan Turai kuma lamari ne na tarihi da ba tantama game da shi.

A cikin bayanin nasa Schröder ya kara da yin nuni da cewar ko da yake gwamnatinsa ba ta samu kafar shigar da dukkan bukatunta ba, amma ta gamsu da sakamakon da aka cimma, musamman ma dangane da maganar tagwaita kuri’ar kasashen da suka fi yawan jama’a a tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai (KTT). Wannan manufa tana da muhimmanci ga Jamus kuma a saboda haka ta amince da ta janye daga bukatarta ta neman kujeru uku a majalisar Turai tun daga shekara ta 2009. Muhimmin abu ga shugaban gwamnati Gerhard Schröder shi ne kasancewar daftarin ya samu amincewar illahirin kasashen KTT. Ya ce kowane daga bangaren da lamarin ya shafa ya nuna halin sanin ya kamata domin cimma wata manufa mai sassauci a tsakani. A nata bangaren shugabar ‚yan Christian Union Angela Merke tayi batu a game da wani ci gaba na tarihi, amma sai ta kara da korafi game da rashin danganta daftarin tsarin mulkin da wata manufa ta addini. Bisa ga ra’ayinta wannan maganar tana da muhimmanci domin bayyana tushen akida da al’adun kasashen Turai a duk wata rawar da kungiyar tarayyar Turai zata taka a siyasar duniya. Ita ma jam’iyyar FDP tayi marhabin lale da daftarin tsarin mulkin, ko da yake kakakinta a majalisar dokoki ta Bundestag Wolfgang Gerhard ya ce daftarin tsarin mulki kawai ba zai tsinana kome wajen kusantar da al’ummomin kasashen kungiyar da juna ba. Akwai bukatar daukar nagartattun matakai game da wannan manufa da kuma bin manufofi bai daya a dangantakun kasa da kasa. Shi ma shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya bayyana goyan bayansa game da karfafa cude-ni-in-cude-ka tsakanin illahirin al’umar kasashen KTT da kuma neman goyan bayansu ga daftarin tsarin mulkin. An kuma saurara daga bakin ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yana mai tsokaci da cewar tilas ne fa illahirin kasashen kungiyar su albarkaci kundin tsarin mulkin kafin ya fara aiki kuma wannan manufa ce da zata iya daukar sama da watanni goma sha biyu masu zuwa. Ko da yake a nan Jamus majalisar dokoki ce zata albarkaci kundin kai tsaye, amma a sauran kasashe da dama na kungiyar tilas ne jama’a su kada kuri’ar raba gardama kansa tukuna.