1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Sana'ar kamun kifi a gargajiyance a Sao Tome

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna MARAPA a tsibirin Sao Tome da principe na kokarin ganin sana'ar kamun kifi irin ta garagajiya ta samu dorewa, tare da magance gurbacewar muhalli

MARAPA kungiya ce mai zaman kanta  a tsibirin Sao Tome da principe wadda ke kokarin koyawa masu sana'ar kamun kifi yadda zasu adana kifi kafin su sayar, kungiyar  ta bada tabbacin cewar kashi 90% na kifin da ake kaiwa kasuwa a tsibirin an kamo sune ta hanyar suu irin na gargajiya. Sana'ar da kusan  mutane 30,000 suka dogara da ita don bukatun su na yau da kullum. Francisco de Santos wani mutum ne da ya shafe sama da shekaru 30 yana kamun kifi.

Ya ce "da idan na fita suu cikin awa 2  na kan kamo kifin da zamu ci kuma mu sayar don samun kudin da zan sayo wasu abubuwan da za a yi amfani dasu a gida ,amma yanzu sai mu fita suu muyi awa 3 ko 4 a cikin teku bamu kamo komai ba".

Ita dai kungiyar MARAPA ta dau aniyar kare halittun cikin ruwa da kuma kara mayar da sana'ar kamun kifin irin ta gargajiya  sana'a mai riba sosai. Elisio Neto masanin halittun cikin ruwa ne a cikin kungiyar. Ya bayyana wa masu kamun kifi muhimmanci amfani da fatsar kamun kifin da ta da ce:

"Wannan shudiyar fatsar mai tsawon mita 40 zababbiya ce,duk kifin da ya shiga cikin ta zai iya fita banda wanda ya isa a kama,amma wannan fatsar guda 2,jama'a in kuna son sana'ar nan ta dore to ku daina amfani da irin wannan".

Masanin tattalin halittun ruwa Elisio Neto ya koya wa sawu 'yan kungiyar masu sayar da kifi a garin Nevas kilomita 30 daga tsibirin Sao Tome, matakan adana kifi kafin a kai kasuwa yadda ba zai lalace ba ta hanyar wanke shi da farko sannan a saka shi cikin ruwan Kal da Gishiri.

Sauti da bidiyo akan labarin