1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sana'ar gashin nama na musamman a Afirka ta Kudu

Leonie March/YIAugust 17, 2016

Max Mqadi mai saida nama a wani dan teburin kasuwancinsa ya habaka har ya kai ga yin wani kamfani wanda ya yi wa lakabi da suna Max's Lifestyle.

https://p.dw.com/p/1Jjjh
Grill- und BBQ Meisterschaft in Fulda
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Welz

Shisa Nyama kalma ce da 'yan Afirka ta Kudu ke amfani da ita wajen kwatanta gashin nama mai dadi. Hakan ne yasa wani mutum mai suna Max Mqadi mai saida nama a wani dan teburin kasuwancinsa ya habaka har ya kaiga yin wani kamfani wanda ya yi wa lakabi da suna Max's Lifestyle a turance a wani gari Umlazi a kasar ta Afrika ta kudu inda yake dafa wani nama mai kyau musamman don Turawa mazauna kasar da ma masu zuwa yawan buda ido a kasar dan faranta masu rai.

Shi dai wannan wurin saida nama ya samu karbuwa sosai ga wadannan al'umma da ke zuwa suna saye ganin irin yadda aka kawata wurin da ababe dabam-dabam. Max Mqadi shi ne mai wannan wuri wanda kuma ya samu nasarar kasuwancinsa sosai ta hanyar yin aiki tukuru kamar yadda ya bayyana.

Ya ce: "Lokacin da na fara na fara ne da wani dan teburi amma yanzu kusan shekaru 15 ke nan. A da mutane sai dai su zo ranakun karshen mako su sai naman. Shi yasa na ga cewa ya kamata in habaka wurin yadda zai dace da bukatar jama'a. Shi yasa na yi kokarin habaka wurin har ya kai haka."

Kalubale kafin harkar ta bunkasa

Mqadi dan shekaru 45 yana matukar alfahari da irin cigaban da ya samu na inganta wannan wurin saida nama kamar yadda ya bayyana.

Ya ce: "Ni ba komai ba ne, kuma ban fito daga wani sanannen wuri ba. Hasali ma babu wanda ya damu da ni a da ganin ba ni da komai. Shi ya sa nike daraja dan Adam saboda kowa da irin darajar da Allah Ya yi masa, don kowa ba ka san abunda zai iya zama ba gobe. Shi ya sa idan kai mai kudi ne tun asali ba za a cika ganin kyamarka ba, saboda da ma tuni an riga an sanka, amma ka ga ni ba komai ba ne, amma sai ga shi na samu gagarumar nasara. Amma fa na fuskanci kalubale dabam-dabam kuma na sha fama kafin gurin ya tsaya da diga-diginsa."

Grill- und BBQ Meisterschaft in Fulda
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Welz

Sai dai dan kasuwar ba wai yana gudanar da kasuwancin don cigaban kasa kadai ba ne, a'a yana taimakawa wajen cigaban al'ummar yankinsa. Don akalla ya dauki ma'aikata 80 kuma ya dauki masu kula da wurin ta fannin tsaro gami da masu kula da inda ake ajiye motocin masu zuwa yin sayayya a wurin.

Jama'a kan je su sai naman kuma a kan kunna sautin wakoki iri dabam-dabam don nishadantar da masu sayan naman.

Himma ba ta ga rago

Mqadi ya kuma kara bayyana dalilan samun nasararsa.

Ya ce: "Samun nasarar da na yi ba ya rasa nasaba da irin yadda mutane ke son irin naman da nike saidawa. Ka ga dai yadda Turawa ke zama suna cin abinci a kwano daya saboda an samamasu abunda ya yi dai-dai da irin al'adar da suke sha'awa kuma ka ga akwai mutanen kasar Holland da Jamusawa a nan wurin."

Ita dai sana'ar koma wacce iri ce ba ta san gaugawa. Masu iya magana dai kan ce tafiya sannu-sannu kwana nesa, kuma mai hakuri shi kan dafa dutse har ma ya sha romansa.