1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sana'ar acaba a Saliyo

Yusuf Bala Nayaya
December 7, 2016

Yayin da ayyukan ‘yan acaba ko okada ke zama wani bangare na rayuwar manyan birane a kasashen Afirka ta fannin zirga-zirgar ababen hawa, wasu na musu kallon masu tada zaune tsaye.

https://p.dw.com/p/2Tv8e
Sierra Leone - Motorräder und Verkehr
Tallafi ga masu sana'ar acaba ko okada a SaliyoHoto: DW/S. Schmidt

To ganin hakan ya sa wasunsu na kafa kungiyoyi domin yin aikinsu da tsafta, kuma har sun samu dama cikin irin ayyukan kungiyar EU na tallafawa kungiyoyi, kasancewar har da irin kungiyoyin 'yan acaba ko kuma okada a birnin Freetown na Saliyo na samun wannan tallafi. Hayaniya da karar motoci da babura abu ne da ya zama wani bangare na birnin na Freetown a kasar Saliyo baya garashin kyawu na hanyoyi, wannan kan sa babura su kutsa lunguna da sakuna na birnin dan kai masu bukata. Ibrahim Thulla dan okada ne wanda kuma ke jan ragamar kungiyar ‘yan acaba a birnin ya ce aikinsu na da muhimmancin gaske ga kasar. 'Yan okada ko acaba kimanin 140.000 ne a  fadin titunan Saliyo, sana'ar da ta yi kaurin suna da kasancewa aiki na tsofaffin masu laifi. Shi ma dai Thulla gabanin karshen yakin basasa na kasar Saliyo a shekara ta 2002, ya taba daukar bindiga cikin yaran sojoji, lokacin da aka kama shi yana da shekaru 14 kafin daga bisani ya kubuta, sai dai a cewarsa wariya da kyama da ake nuna musu ba ta dace ba kuma wannan batu ai tsohon labari ne.

 

A da idan ana musguna musu ko rikici da 'yan sanda masu cin hanci a birnin, basu da wata hanya face su hau tituna da zanga-zanga, sai dai kungiyar Tarayyar Turai cikin aiyukan agaji da take a wannan kasa ta Saliyo ta ware kudi Euro 300,000 dan ayyukan bada horo ga shugabannin kungiyoyi na sa kai, kuma ita ma kungiyar ta 'yan okada ko acaba ba a barta a baya ba wajaen samun fadakarwa daga kungiyar ta EU. Shi dai Thulla da irin wayewar kan da ya samu a irin wannan fadakarwa yana son ganin lamura na tafiya bisa doka, kana yana da buri na karatu a fannin kimiyar siyasa sannan ya na so ya ci gaba da wannan sana'a tasa yanzu. Kungiyar Tarayyar Turai dai na da buri na samar da wasu ayyukan raya kasa a Saliyo, daya daga cikin ayyukan da ta maida hankali shi ne na ganin bin doka da oda ya samu gindin zama kana ungiyoyin al'umma su yi karfi, gwamnati ta samu iko wajen yin huldodinta. A saboda haka kungiyar ta kudiri aniya ta ayyukan kudi da ya kai Euro miliyan 25 zuwa wannan kasa da ke a yammacin Afirka nan da shekara ta 2020.