1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Burtaniya ta bada sammaci akan Tzipi Livni

December 16, 2009

Israela ta yi Allah wadai da sammacin da ƙasar Birtaniya ta bayar na a kamo tsohuwar ministar harkokin wajen ƙasar Zipi Livni

https://p.dw.com/p/L3fa
TsohuwarMinistar harkokin wajen Israila Tzipi LivniHoto: AP

Israela ta yi Allah wadai da sammacin da ƙasar Birtaniya ta bayar na a kamo tsohuwar ministar harkokin wajen ƙasar Zipi Livni. Wannan Sammacin ya tada hankalin mahukuntan Israela, inda suke jin tsoron cewa hakan zai hana jami'anta fita daga ƙasar.

Da yake mai da martani muƙaddashin Firayim ministan ƙasar Yahuduwa Silvan Schalom ya bayyana cewa wannan matakin da kotun ƙasar Birtaniya ta ɗauka, na kamo tsohuwar ministar ta harkokin waje rashin fahimta ce ta yadda al'amura suke.

"A wannan lamarin dukkan mu Zipi Livni ne, Wannan bita da ƙullin ba za ta saɓu ba. Dole mukare kanmu daga masu neman shiga harkar mu"

Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta miƙawa jakadan ƙasar Birtaniya koken ta, kuma Israela tace mahukuntan London zata ɗorawa laifin barin kotu ta ɗau wannan makin. Yanzu haka dai Yahudawa sun ɗauki wannan sammacin da zafin gaske. Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Israela ya ƙira gwamnatin Birtaniya, da ta soke wannan ayar doka, dake bada umarnin a kama mutanen da sukayi laifi a wajen ƙasar.

Wannan lamarin zai ƙara kawo ɓaraka a danƙantakar Israela da Birtaniya, idan akayi misali da yadda jami'an Israela suke ta kumfar baka a bisa sammacin.

Israelische Kampfverbände beschießen den gaza-Streifen
Daya daga cikin tankokin yaƙin Iraila a lokacin da suke luguden wuta akan GazaHoto: AP

Ita dai Zipi Livni, wadda take a matsayin ministar harkokin wajen Israela a loakcin da sojin ƙasar suka ƙaddamar da yaƙi a kan Zirin Gaza, ta yi ƙaurin suna ne sakamakon yadda ta fito ta yi ta kare kisan Falasɗinawa da sojojin suka yi "muna cikin kwana 16 na ƙaddamar da farmaki, kuma za mu cigaba, kana wannan shine abu mafi dacewa, kuma ina so na faɗa, mune kawai zamu ɗau matakin janye dakarun mu, babu wani mahluƙin da zai samu janye"

A wancan lokacin dai sojojin Israela sun hallaka Palsɗinawa kimanin1400. Daga bisani ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta yi bincike, kuma ta fidda rohoto wanda yace sojin Israela sun aikata laifin yaƙi, domin kisan gillar da suka yiwa Palasɗinawa fararen hula.

Zipi Livni dai ada ta shirya hallatar taron Yahudawa da za'a gudanar a birnin London ranar Lahdi mai zuwa, amma yanzu tana isa Lodon za'a cafketa, abinda kuma ya tilas ta mata zama a gida. A yanzu babu ita babu ficewa daga gida, sai dai kawai madugar adawan a Israela tayi ta lissafi na irin dokokin ƙasar Birtaniya.

Mawallafa : Engelbrecht Sebastian / Usman Shehu Usman

Edita : Abdullahi Tanko Bala